Kun taba ganin koci mace bahaushiya?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Kun taba ganin koci mace Bahaushiya?

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin da Fauziyya Kabir Tukur ta gabatar:

Ba kasafai a ke ganin kociyan ‘yan wasa bahaushiya ba.

Haka ba ya rasa nasaba da al’ada, ganin cewa ko ‘yan wasa ma, mafi yawansu maza ne.

To sai dai Aisha S Dauda ta zama abun kwatance a fagen wasan kwallon kwando inda ta yi yayinta a matsayin ‘yar wasa kuma daga bisani ta zama kociya.

Soyayya da kwarewarta a kwallon kwando ya sa ta dauki wannan mataki, kuma a yanzu ta horar da gomman yara maza da mata a wasan.

Fauziyya Kabir Tukur ta tattauna da ita kan abunda ya ja ra’ayinta ta shiga harkar wasan da kuma yadda ta fara horar da yara ‘yan wasa.

Ta kuma bayyana nasarori da matsalolin da ke tattare da horar da ‘yan wasa a Najeriya.

Labarai masu alaka