Khashoggi: Turkiyya ta ce an narkar da gawarsa a cikin asid'

jamal khashoggi

Asalin hoton, Getty Images

Wani babban jami'in Turkiyya, mai bai wa shugaban kasa shawara Yasin Aktay ya ce ya yi imanin cewa an narkar da gawar dan jaridar nan na kasar Saudiyya Jamal Khashoggi da sinadarin acid bayan kashe shi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin Santanbul.

Mr Aktay, wanda mashawarci ne ga Shugaba Erdogan, ya ce wannan shi ne kawai abin da za a iya fahimta daga wannan dambarwar, cewa wadanda suka kashe dan jaridar sun lalata gawarsa ne saboda kar su bar wata alama da za a gano su.

Khashoggi, wanda yake yawan sukar masarautar Saudiyya, ya kasance a ofishin jakadancin kasar a ranar 2 ga watan oktoba.

Sai dai babu wata hujja da aka samu daga sakamakon binciken kwa-kwa da ke nuna cewa an narkar da gawar.

Mr Aktay ya shaida wa jaridar Hurriyet Daily cewa "Dalilin da ya sa suka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa shi ne don su narkar da ita cikin sauri."

"Yanzu mun gano cewa ba gunduwa-gunduwa kawai suka yi da gawar ba, har da narkar da ita ma."

Wannan ikirari na zuwa ne a yayin da budurwar Khashoggi Hatice Cengiz, ta yi kira ga shugabannin duniya don su gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

A hannu guda kuma wasu rahotanni sun ruwaito Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman yana shaida wa Amurka cewa ya dauki Khashoggi a matsayin "musulmi mai hadarin gaske."

Kalaman nasa da ya yi ta wayar tarho zuwa ga Fadar White House sun zo ne kafin Saudiyya ta amince cewa an kashe Khashoggi.

Saudiyya ta yi watsi da kalaman ko batun cewa gidan sarautar na da hannu a kisan, ta kuma ce "a shirye take ta gano dukkan gaskiya."

Mai shigar da kara na Santanbul a ranar Laraba ya tabbatar da cewa an shake Mista Khashoggi.

Me aka fada a tattaunawar da ake zargin Yarima mai jiran gado ya yi ta waya?

A yayin da yake tattaunawa ta waya da surukin Shugaba Donald Trump, Jared Kushner da kuma babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro John Bolton, Yarima Mohammed ya ce Khashoggi dan kungiyar 'yan uwa musulmi ne ta Brotherhood, kamar yadda jaridar Washington Post ta ruwaito.

An yi tattaunawar ne a ranar 9 ga watan Oktoba, mako guda bayan bacewar Khashoggi.

An kuma ruwaito Yarima Mohammed ya bukaci Fadar House ta mutunta dangantar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yarima Mohammed ya bukaci Fadar House ta mutunta dangantar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya

A wata sanarwa da suka aikewa jaridar, iyalan Khashoggi sun yi watsi da batun cewa shi dan kungiyar 'yan uwa musulmi ne ta Brotherhood ne sun kuma ce dan jaridar ya sha musanta wannan batu da kansa a shekarun da suka gabata.

"Jamal Khashoggi ba mutum ne mai hatsari ba ta kowace hanya. Ikirarin hakan shirnen banza ne," in ji sanarwar.

Me bincike ya gano zuwa yanzu?

Har yanzu babu wata matsaya kan yadda aka kashe Khashoggi. Ya shiga ofishin jakadancin ne don warware wasu batutuwa kan batun aurensa.

Bayanan bidiyo,

Hatice Cengiz, wadda Jamal Kashoggi za ya aura

Amma a ranar Laraba Turkiyya ta ce an shake shi ne jim kadan bayan shigarsa ofishin jakadancin "cikin shirin kashe shi da aka shirya yi."

Kafofin yada labaran Turkiyya a baya sun ambato wasu majoyoyi cewa Turkiyya tana da muryoyin da ta nada da ke tabbatar da cewa an azabtar da Khashoggi kafin a kashe shi.

Saudiyya ta sauya maganarta kan abun da ya samu Khashoggi.

A karon farko da aka gane ya bata, ta ce Khashoggi ya fice daga ofishin da ransa. Daga baya ta yarda cewa an kashe shi, ta kuma ce kisan ya zo ne sakamakon wani dan hargitsi da ya tashi.

Daga baya ta kama mutum 18 da take zargi, wadanda ta ce a Saudiyya za a yi musu shari'a. Sai dai Turkiyya ta fi so a yi musu shari'a a kasarta.

Asalin hoton, EPA

A makon da ya gabata ne Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi magana da Sarkin Saudiyya Salman, kuma su biyun sun yarda za su hada kai don ci gaba da binciken