Mai shekara 75 ya kashe kansa bayan ya fada tekun Lagos

man lagoon
Bayanan hoto,

Masu ninkaya sun tsamo gawarsa bayan sa'a guda da fadawarsa

Wani dattijo mai shekara 75 mai suna Oladejo O.R, ya kashe kansa ta hanyar fadawa cikin teku a birnin Legas a Gadar Third Mainland da safiyar Juma'a.

A kwanan ne mutumin ya yi ritaya daga aikin gwamnati a Rediyon Tarayyar Najeriya FRCN.

Wani abokin aikinsa Yemisi Nubi, da ke tare da shi a lokacin da lamarin ya faru, ya shaida wa BBC cewa suna wata tattaunawa ce mai taba rai sai marigayin Oladejo ya ce masa ya tsayar da motar don yana so ya yi bawali.

"Kawai sai ya bude kofar motar ya zunduma cikin tekun, in ji Nubi.

Daya matar da ke cikin motar Ajanaku Aina, wadda mataimakiyar darakta ce a FRCN, ta shaida wa BBC cewa marigayin direbanta ne.

"Kwanan nan ya yi ritaya sai na dauke shi don ya zama direbana. Ya zo aiki da safiyar yau (Juma'a), sai na ce masa ba sai ya tuka motata ta wajen aiki ba saboda za mu tafi tare da Yemisi," in ji Aina.

Bayanan hoto,

Uwardakin marigayin na cikin alhini

Oladejo ya yi aiki da FRCN a matsayin direba.

"Ban san me ya sa ya aikata hakan ba. Har yanzu bai karbi kudin fanshonsa ba. Yana dai sa ran karbar. Me ya sa zai kashe kansa," in ji Nubi.

Masunta a yankin da masu ninkaya da ke kusa lokacin da abun ya faru sun gano gawar Oladejo, sa'a daya bayan fadawarsa tekun.

Jami'an Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas ce ta tabbatar da mutuwarsa.

Kashe kai ta hanyar fadawa teku a Legas ya zama ruwan dare.