NAFDAC ta haramta cin Kifi 'Pufferfish' a Najeriya

Kifi mai guba Pufferfish

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

NAFDAC ta ce tana tunanin an shigo da kifin mai dauke da guba a Najeriya

Hukumar NAFDAC da ke kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta yi wani babban gargadi ga 'yan kasar game da kaucewa cin wani nau'in kifi da ake kira Pufferfish a turance saboda illarsa ga lafiya.

Hukumar ta bayyana cewa jikin kifin na dauke da wani dafi mai guba da zai iya haifar da rashin lafiya mai tsanani ga jikin dan adam, kuma wannan ne dalilin da ya sa ta haramta cinsa.

Hukumar ta ce alhakinta ne ta sanar da 'yan Najeriya game da hatsarin da ke tattare da cin kifin wanda ba a riga an san shi ba a kasar.

An fi yawan cin kifin a kasashen yankin Asiya kamar Japan da China da yankin Koriya a cewar hukumar.

Mista Sherif Olagunju, babban jami'n hukumar NAFDAC da ke kula da bangaren kiyaye abinci mai kyau da mai gina ciki ya ce sun samu labarin hatsarin da ke tattare da cin kifin daga wasu da suka ci a wasu kasashen Afrika.

"Saboda rigakafi ta fi magani ya sa muka ga ya dace mu yi gaggawar yin gargadi," in ji shi.

Ya kuma ce suna tunanin an shigo da kifin a Najeriya daga waje amma ya jaddada cewa ba wanda hukumarsu ta ba izinin shigo da kifin.

"Mun san mutane ba su da masaniyar haka, dalilin da ya sa muka yi gaggawar yin wannan gargadi ga jama'a domin kauracewa cin kifin domin wasu na iya cewa ana magani da shi."