Me ya sa Atiku da Buhari 'suka raba kan 'yan Kannywood'?

Mun zabo hotunan wasu daga cikin 'yan Kannywood da ke goyon bayan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wadanda ke mara wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar baya a fafutukar da suke yi wajen ganin sun ci zaben 2019.

Sani Musa Danja

Asalin hoton, Twitter/Sani Danja

Bayanan hoto,

Sani Musa Danja shi ne kan gaba a cikin 'yan Kannywood da ke jam'iyyar PDP kuma yana goyon bayan Atiku Abubakar

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

A yayin da Adam A Zango ke goyon bayan Shugaba Buhari...

Asalin hoton, Instagram/Nasiru Horo Dan-mama

Bayanan hoto,

...an hango yaronsa, Nasiru Horo Dan-mama, yana tallata tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

Asalin hoton, InSTAGRAM/Aminu Saira

Bayanan hoto,

Malam Aminu Saira na tare da Buhari...

Asalin hoton, fACEBOOK/Bashir Nayaya

Bayanan hoto,

... shi kuwa Bashir Nayaya(dama) ya ce 'Sai Atiku!', ko da yake ba a san inda Sarki Ali Nuhu ya sa gaba ba

Asalin hoton, Facebook/Nigeria presidency

Bayanan hoto,

Fati Washa na cikin 'yan Buhariyya!

Asalin hoton, InSTAGRAM/Fati mUhd

Bayanan hoto,

Fati Muhammad ta dade tana tallata Atiku

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

...Amma Ado Gwanja ya ce kuri'arsa na wurin Buhari

Asalin hoton, InSTAGRAM/MARYAM BOOTH

Bayanan hoto,

...ko da yake Maryam Booth ta ce sai ta tabbatar Atiku ya zama shugaban Najeriya