Rikicin 'yan Shi'a: Sojin Nigeria 'sun yi amai sun lashe'

'Yan Shia sun ce ba za su gaji da zanga-zanga ba Hakkin mallakar hoto Twitter/@imnig_org
Image caption 'Yan Shia sun ce ba za su gaji da zanga-zanga kan a saki El-Zakzaky ba

Rundunar sojin Najeriya ta goge wani bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump wanda ta kafa hujja da shi wuri bude wa 'yan Shi'a wuta.

A cikin bidiyon, Shugaba Trump ya ce sojoji za su iya amfani da karfi kan baki 'yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.

"Idan suka yi jifa da duwatsu... ku dauka sun yi da bindiga ne," in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.

Jami'an tsaron Najeriya sun ce mabiya Shi'a uku sun mutu a wani mummunan artabu tsakaninsu na tsawon kwanaki a Abuja.

ko da yake mabiya Shia sun ce an kashe musu kusan mutum 50.

Hujjar da sojin suka kafa da bidiyon Mr Trump ta jawo musu mummunar suka daga bangarori da dama na al'uma.

Watakila hakan ne ya sa ranar Juma'a rundunar sojin ta goge sakon bidiyon ko da yake ba ta fadi dalilinta na daukar matakin ba.

Gabanin goge bidiyon, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki sojojin kasar da kashe 'yan Shi'a, inda kuma ta ce zanga-zangar 'yan Shi'ar ta lumana ce.

Sai dai mai magana da yawun sojojin kasar Burgediya Janar John Agim ya ce sun yi amfani da harsasai masu rai ne ga masu zanga-zanga saboda suna dauke da makamai.

Ya ce: "Wannan ne abin da Mista Trump yake magana a kai."

Amurka na so a yi bincike

Shafin Twitter na rundunar sojin kasar ya wallafa bidiyon Shugaba Trump da rubutu kamar haka: "kalli wannan bidiyon, ka yanke hukunci".

Kakakin sojin ya ce sun wallafa bidiyon ne saboda mayar da martani ga rahoton kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suke cewa sojoji sun yi amfani da makami kan 'yan Shi'a masu zanga-zanga.

Sai dai rundunar sojin ba ta yi magana game da sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar ba, inda Amurka ta bukaci gudanar da cikakken bincike da hukunta masu laifi a rikicin.

Ba za a iya tabbatar da yawan 'yan Shi'an da sojojin kasar suka kashe a Abuja lokacin artabun da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi ba.

Sojoji sun ce mutum shida ne suka rasa rayukansu, amma 'yan Shi'an sun ce adadin ya wuce haka nesa, ita kuma kungiyar Amnesty ta ce adadin ya kai kimanin mutum 45.

Rikicin ya fara ne a lokacin da 'yan Shi'ar suka fara tattakin Arbaeen na shekara-shekara a Abuja - wato tarukan tunawa da kisan jikan Manzon Allah (SAW).

Har ila yau 'yan Shi'an suna neman sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ake tsare da shi kimanin shekara uku ke nan, bayan wani rikici da kungiyar ta yi da sojoji a Zaria.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro sun ce rikicin ya fara ne bayan da masu zanga-zangar suka yi kokarin karbe iko da wani shingen bincike

Labarai masu alaka