Unguwar da yara ke makancewa a Abuja
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Unguwar da yara ke makancewa a birnin Abuja

Dubban mutanene ke zaune a wata unguwa da ke wajen babban birnin Najeriya Abuja, sai dai jama'ar yankin na fama da cututtuka dake makanta yara sakamakon rashin ruwa mai tsafa.

Rashin ingantaccen ruwa sha shi ne babbar matsalar yankin na Ruga, sai kuma matsalar rashin bandakuna da rashin tsaftar muhalli.

Matsalolin suna haifar da cututtuka musamman ma makanta ga kananan yara, wacce take naksa su tun suna kanana.

Labarai masu alaka