Kun san inda ake tilasta wa ma'aikatansa shan fitsari da cin kyankyasai?

Cockroach on a fork Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Duk ma'aikacin da ya gaza, sai ya cika cikinsa da wannan

An daure wasu manajojin wani kamfani a China domin sun tilastawa wasu ma'aikatansu shan fitsari da cin kyankyasai.

'Yan sanda sun dauki mataki bayan da wani bidiyo ya bayyana inda ake nuna ana dukan wasu ma'aikata da bel, kana suna shan wani abu mai launin ruwan kwai.

An kuma wallafa wasu labarai a shafukan sada zumunta da ke cewa an rika sa ma'aikatan su ci kyankyasai idan suka gaza cimma bukatar da kamfanin ya dora masu.

An daure manajoji uku na tsawon kwanaki biyar zuwa 10 saboda wannan laifin, kamar yadda jaridar South China Morning Post ta ruwaito.

Wani bidiyon da aka wallafa a shafin sada zumunta na China, Weibo, ya nuna lokacin da ake dukan wani ma'aikaci da bel bayan an tilasta masa tsaya a tsakiyar kawanyar abokan aikinsa.

Hakkin mallakar hoto Pearvideo.com
Image caption Wannan bidiyon ya ja hankula sosai a Weibo

An nuna wasu ma'aikatan kuma na shan wani abu mai launin ruwan kwai a kamfanin gyaran gida da ke birnin Guizhou, kuma sun rika toshe hancinsu a yayin da suke shan abin.

An kuma nuna hotunan wasu sakonni da aka ce manajojin kamfanin ne suka rubuta, wadanda aciki suke gargadin ma'aikatansu cewa za su ci kyankyasai idan ba su kara kwazo ba.

Kamar yadda wasu arahotanni suka bayyana, an rika horas da ma'aikatan ta hanyoyi daban-daban, kamar sanya su su sha ruwan masai, ko aske masu gashin kansu gaba daya.

Hakkin mallakar hoto Pearvideo.com
Image caption Rahotanni na cewa wannan abin mai launin ruwan kwai fitsari ne

An kuma ce kamfanin ya kasa biyan ma'aikatansa albashinsu na wata biyu kuma ma'aikatan na tsoron kwarmata batun domin za su rasa kudaden idan suka ajiye aiki.

Labarai masu alaka