An sako daliban da aka sace a yankin Bamenda na Kamaru

the school where they were kidnapped Hakkin mallakar hoto Evn
Image caption An sace daliban ne daga wannan makarantar sakandaren da ke Bamenda

An sako daliban da aka sace daga wata makarantar kwana a yankin kudu maso yammacin Kamaru.

An sace daliban, su 78 da wasu mutum uku da safiyar Lahadi a babban birnin Lardin na Bamenda.

An kuma sako wani direba, amma har yanzu ba a sako shugaban makarantar da wani malami ba.

Gwamnati da 'yan aware a yankin mai amfani da harshen Ingilishi sun rika nuna wa juna yatsa, inda suke dora laifin sace daliban akan junansu.

Wani bidiyo da aka ce na nuna wasu daga cikin daliban da aka sace daga makarantar sakandare ta Presbyterian na ta yawo a shafukan intanet ya janyo damuwa matuka.

Yankin mai amfani da harshen Ingilishi na kokarin ballewa daga kasar ta Kamaru, a kasar da masu amfani da harshen faransanci suka fi yawa.

Har yanzu ba a san ko su wane ne suka sace daliban ba, kuma ba a san dalilinsu na yin haka ba. Amma hukumomi sun ce ana tambayar daliban kafin a mayar da su ga iyayensu.

Ta yaya aka sako daliban?

Cocin Presbyterian na Kamaru ya ce an yashe yaran ne a wani gini da ke garin Bafut, wanda ke da nisan kilomita 24 daga birnin Bamenda.

"'Yan bindigan da suka sace su sun sako su cikin sauki da kwanciyar hankali. Daga nan sai aka kawo su zuwa harabar cocinmu", inji Rabaran Fonki Samuel, wanda shi ne jami'i mai kula da harkokin cocin Presbyterian na makarantar a yayin wata hira da yayi da shirin rediyo na Newsday na BBC.

"Bayanan farko da muka samu daga wadanda suka sace daliban shi ne sun kira mu ta wayar tarho suna cewa suna son sako yaran jiya (Talata) da safe...amma an tafka ruwa sosai, wanda shi ya hana a sako sun."

Ya kara da cewa, "Amma da yammacin jiya Talata, kuma cikin ikon ubangiji, sai kawai a ka dawo mana da yaran."

Cocin Presbyterian din kuma ya bayyana cewa satar daliban na Lahadi shi ne karo na biyu da aka sace yaran makarantar a kasa da mako guda.

A ranar 31 ga watan Oktoba, an sace wasu daliban makarantar 11, amma aka sake su. Ba a san ko suwa ne ne suka sace yaran ba.

Image caption Yankunan arewa maso yamma da kudu maso yamma sune na masu amfani da harshen Ingilishi a Kamaru

Ministan sadarwa Issa bakary Tchiroma ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "an sako dukkan dalibai 79", amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Hukumomi sun baza sojojin kasar domin nemo daliban.

Su waye su ka sace daliban?

Rabaran samuel ya fada wa BBC cewa bai damu da sanin wadanda suka sace yaran ba, sai dai yana "cike da murna da farin ciki" cewa an sako su.

Hukumomin Kamaru sun dora laifin sace yaran a kan 'yan awaren yankin rainon Ingila - wadanda suke kamfen cewa a rufe dukkan makarantun da ke yankin.

Suna son samar da kasa mai cin gashin kanta da suka ba sunan Ambazonia.

Me ke faruwa a yankin rainon Ingilishi na Kamaru?

Yankuna masu amfani da harshen Ingilishi na Kamaru sun dade suna kokawa da yadda suka ce ake nuna masu bambanci a kasar.

Sun ce ana nuna masu wariya a ayyukan gwamnati kuma akan wallafa takardun gwamnatin a harshen Faransanci duk da cewa Ingilishi ma na cikin harsunan kasar a hukumance.

Kamaru - har yanzu kawuna basu hadu ba

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Turawan mulkin mallaka ne suka "tsaga" nahiyar Afirka zuwa kasashe domin amfaninsu
  • Jamus ta mulki Kamaru a shekarar 1884
  • Sojojin Birtaniya da Faransa sun fatattaki Jamusawa a 1916
  • Bayan shekara uku an raba Kamaru gida biyu - kashi 80 cikin 100 na Faransa, kashi 20 cikin 100 kuma na Birtaniya
  • Yankin da ke karkashin ikon Faransa ya sami 'yanci a 1960
  • Bayan zaben raba gardama, yankin Kudancin Kamaru ya hade da Kamaru, inda yankin Arewacin Kamaru ya hade da Najeriya mai amfani da harshen Ingilishi.

Labarai masu alaka