Cutar Ebola na ci gaba da zama barazana - WHO

Jami'an lafiya
Image caption Ko a makwannin da suka gabata sai da aka yi wa jami'an lafiya allurar riga-kafin cutar Ebola a kasar

Shugabannin hukumar lafiya ta duniya da hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira a girke sojoji a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo don bunkasa tsaro yayin da kasar ke fama da barazanar cutar Ebola.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce cutar na ci gaba da yin barazana ga rayuwar jama'a.

Shi ma babban mai kula da ayyukan jin kai da tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Jean-Pierre Lacroix, yana fatan za a shawo matsalar tsaro a kasar musamman birnin Beni wadda ita ce cibiyar cutar Ebola.

Sama da mutane 300 ne suka kamu da cutar, kuma kimanin 190 suka mutu, an kuma killace sama da 5000 a gabashin Congo bayan sake barkewar cutar.