An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka

The 19 women were elected to county judgeships on Tuesday An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka a ranar Laraba Hakkin mallakar hoto Harris County Democratic Party
Image caption An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka a ranar Talata

An kafa tarihi a ranar Talata bayan da aka zabi mata 19 a matsayin alkalai a birnin Houston na jihar Texas.

Wannan nasarar da matan suka samu ta kawo farin ciki a jihar musamman a kafofin sada zumunta.

Wani hoton matan, wanda ake kira Houston 19, wanda aka dauka a watan Agusta ya karade shafin sada zumunta na Twitter.

LaShawn A Williams ya wallafa hoton a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa: "Ban taba tunanin ranar da zan yanke shawarar neman takarar alkali ba, har da zan zama daya daga cikin jarumai mata, surukai, ma masu fasaha, jarumai - duk abin da nake fata na kasance! "

Ta amfani da maudu'in #Houston19, mutane da yawa sun yi murnar zaben jami'an.

Yankin Harris na da adadin mutane miliyan hudu da rabi, kuma shi ne mafi girma a jihar Texas, kuma na uku mafi girma a Amurka.

Labarai masu alaka