An daure Malamin 'tsubbu' kan kudin jabu a Kano

dala Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata kotun tarayya da ke Kano a Najeriya ta yi wa wani mutum mai suna Abubakar Ishak da aka fi sani da Mairakumi daurin shekara 10 a gidan kaso, bayan ta kama shi da laifin rike jabun kudin takardun dalar Amurka.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, wato EFCC ce ta gurfanar da Abubakar Ishak Mairakumi a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Lewis Allagoa, ta tuhume shi da aikata laifuka biyu, ciki har da mallakar kudin jabu na takardun dalar Amurka guda 176.

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, wato NDLEA ce ta fara kama Malam Mairakumi da takardun kudin jabun lokacin da ta kai wani samame a gidansa, sannan daga bisani ta danka shi ga hannun hukumar EFCC.

Bayan Malam Mairakumin ya amince da aikata laifin, kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar a kan kowace tuhuma ba tare da ba shi zabin tara ba - wato shekara 10 ke nan.

Amma zai ci zaman gidan mazan na hukuncin tuhuma biyun ne lokaci guda. Don haka zai shafe shekara biyar ke nan a dunkule.

Sai dai bayan hukuncin kotun tarayyar, wanda aka yi wa daurin yana da damar daukaka kara.

Bayan umarnin da ta bayar na iza keyar Malam Mairakumin zuwa gidan yari, kazalika kotun ta ba da umarnin cewa a lalata dalolin Amurka na jabun da aka kama a hannunsa.

Abubakar Ishak Mairakumi dai kan yi ikirarin malanta da kan taimaka da addu'o'i, wanda akansa tallarsa a gidajen rediyon a jihar Kano, amma kuma wasu na zargin cewa dan damfara ne, duk kuwa da cewa yana musanta hakan.

Labarai masu alaka