An kai mummunan harin bam a birnin Mogadishu

Somalia Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akalla mutum 17 ne suka mutu bayan wani harin bam da aka kai Mogadishu, babban birnin Somaliya a ranar Juma'a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

"A yanzu dai muna da tabbacin cewa fararen hula guda 17 ne suka rasa rayukansu. Harin ya rutsa da su ne lokacin da suke tafiya a cikin motocin haya. An yiwuwar adadin mutanen da suka mutu ya karu," in ji wani jami'in dan sanda Ali Nur.

Ya ce wadansu 'yan kunar bakin wake ne suke alhakin kai wannan harin a wani otel da ke kusa da hedkwatar sashen binciken manyan laifuka na 'yan sanda kasar (CID).

Masu aikin tsaron otel din Sahafi, inda aka kai harin da kuma 'yan sanda sun bude wuta bayan da bama-baman suka fashe a cikin wata mota a kusa da otel din da kuma ofishin CID, a cewar rahotanni.

Bayan minti 20 da kai harin farko, wani bam ya sake tashi a wani titi mai cinkoson jama'a.

Wani jami'in dan sanda ya shaida wa kamfanin Reuters cewa mutum 17 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar harin, amma kamfanin dillancin labaran ya ce mai daukan hoton su ya kirga gawawwaki 20.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hari, amma a baya kungiyar al-Shabab ta sha daukar alhakin kai irin wannan hare-hare.

Labarai masu alaka