Turkiyya ta yada bidiyon kisan Jamal Khashoggi

Jamal Khashoggi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasar Turkiyya ta bai wa Amurka da Burtaniya da Saudiyya da wasu kasashe bidiyon kisan dan jaridar nan mai sharhi Jamal Khashoggi.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nanata ikirarin da ya yi cewa Saudiyya ta san wanda ya kashe Khashoggi.

Khashoggi, fitaccen mai sukar gidan sarautar Saudiyya ne, wanda aka kashe a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul ranar biyu ga watan Oktoba.

Saudiyya ta amince cewa a ofishin nata aka kashe shi, ko da yake ta ce babu hannun 'yan gidan sarautar kasar.

Tun da fari mahukuntan kasar sun ce dan jaridar ya fita daga ofishin jakadancinsu bayan ya kammala abin da ya kai shi.

Kazalika masarautar Saudiyya ta musanta wasu kalamai da aka zargi Yarima mai jiran gadon sarautar kasar Mohammed bin Salman ya yi inda ya bayyana Khashoggi a matsayin musulmin da ke da matukar hatsari.

An ce ya yi kalaman ne a wata hira ta wayar tarho da ya yi da wani jami'in fadar White House gabanin Saudiyya ta amince cea an kashe Khashoggi.

Har yanzu dai babu wata matsaya daya da ke nuna takamaimai yadda Mr Khashoggi ya mutu. Ya je ofishin jakadancin ne domin karbar wasu takardu game da auren da zai yi.

Da farko dai, wasu kafafen watsa labaran Turkiyya sun ambato majiyoyi na cewa kasar tana da muryoyin da ke nuna cewa sai da aka azabtar da Khashoggi kafin a kashe shi.

Sai dai a makon jiya Turkiyya ta ce an makure dan jaridar ne lokacin da ya shiga ofishin jakadancin sannan aka yi gunduwa-gunduwa da namansa "kamar yadda aka tsara gabanin hakan".

Har yanzu ba a ga gawarsa ba kuma Turkiyya ta ce an sanya ta a cikin sinadarin asid.

Sau da dama Saudiyya tana sauya kalamanta kan yadda aka kashe Khashoggi.

Labarai masu alaka