An yi bikin Deepika Padukone da Ranveer Singh

Ranveer Singh da na Deepika Padukone Hakkin mallakar hoto @ranveersingh

Abin da magoya bayan jarumi Ranveer Singh da na Deepika Padukone suka jima suna jira shi ne batun ganin jaruman nasu wadanda masoyan juna ne sun yi aure.

Yanzu haka dai ta faru ta kare, domin kuwa a ranar 14 ga watan Nuwambar 2018 ne, aka yi bikin jaruman a wajen wani shakatawa da ke Italiya.

An dai yi bikin da baikonsu ne a bisa tsari irin na al'adarsu.

Iyayen Deepika dai sun tarbi iyalan Ranveer a wajen bikin kamar yadda ya ke a al'adance domin gudanar da baikon.

Masoyan junan dai sun yi musayar zobe a tsakaninsu a gaban 'yan uwa da abokan arzikinsu.

Deepika da Ranveer, sun kasance suna tare ne fiye da shekara shida da ta gabata, wato sun fara soyayya ne a lokaicn da suke daukar fim din Ram-Leela.

Soyayyarsu ta kara karfafa ne bayan da suka yi fim din Bajirao Mastani da kuma Padmaavat.

Masoyan junan, sun bukaci duk masu halartar bikin na su da je wajen bikin ba tare da wayoyinsu na salula ba saboda sirri.

Labarin auren jaruman dai na da da jan hankalin mutane a shafukan sada zumunta a kasar dama wasu kasashen duniya.

Labarai masu alaka