An rage wa Joshua Dariye da Jolly Nyame yawan shekarun gidan yari

Tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta rage wa tsohon gwamnan jihar Filato Sanata Joshua yawan shekarun da zai shafe a gidan yari daga 14 zuwa 10.

Mai shari'a Stephen Adah ne ya jagoranci zaman kotun na karar Mista Dariye da aka yi a ranar Juma'a.

Kazalika a wani zaman da kotun ta yi a ranar karkashin mai shari'a Emmanuel Akomaye Agim, ya rage shekarun da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame zai yi a gidan kason shi kuma daga shekara 14 zuwa 12.

Sai dai dukkan tsoffaffin gwamnonin ba su halarci zaman kotun ba, amma lauyoyinsu sun halarta.

Wakilin BBC Sani Aliyu da ya je kotun ya ce masu shari'ar da lauyoyin wadanda ake karar da ma lauyoyin gwamnati babu wanda ya yi bayanin dalilin rashin halartar tasu.

Sannan kotu ta umarci Mista Nyame da ya biya tarar naira miliyan 495.

Zai biya wannan tara ne saboda yadda "ya rika kashe kudin al'umma" kamar yadda mai shari'ar ya ce.

Sai dai kuma ba a gabatar da wannan korafin ba a zaman shari'ar farko da aka fara yi ta tsohon gwamnan.

A ranar 12 ga watan Yunin bana ne wata kotun Tarayya ta zartar da hukuncin daurin shekaru 14 a kan tosohun gwamnan Filato sanata Dariye bayan samun shi da laifukan da suka shafi zamba da almubazzaranci da suka shafi kudi sama da biliyan biyu na Naira a lokacin da yana gwamna.

Kotun ta samu Mista Dariye da laifuka 15 cikin 23 da hukumar EFCC ta gabatar.

A daya bangaren kuma kotu ta samu Jolly Nyame na jihar Taraba da laifuka 27 daga cikin 41 da EFCC ta gabatar da kotu.