Me ya sa gwamnatin Buhari ke so mata su yi tazarar haihuwa?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Me ya sa gwamnatin Buhari ke so mata su yi tazarar haihuwa?

Ku latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren cikakkiyar hira da Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga mata su daina haihuwa barkatai tana mai cewa hakan ba zai yi wa kasar amfani ba.

Ministar kudin kasar Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, wadda ta shaida wa BBC hakan a wata hira ta musamman, ta kara da cewa yawan haihuwar 'ya'yan da mutum ba zai iya kula da su ba yana yin illa ga tattalin arzikin Najeriya.

"Kasarmu muna cikin wani hali da dole kowa ya hada hannu a tayar da tattalin arzikinta.Wani rahoto da babban bankin duniya ya fitar ya nuna cewa a tsaka-tsaki mace daya na haihuwar 'ya'ya bakwai zuwa takwas; idan bamu zauna muka yi wa kanmu fada ba cewa lallai ne kowacce mace idan ta haihu a bar ta lafiyar jikinta ta dawo kafin ta sake yin ciki, muna cutar matar da 'ya'yanta. Za ka ga mace tana da ciki tana da goyo; ita ba koshin lafiya, yaron ba koshin lafiya," in ji Hajiya Zainab.

Ta kara da cewa "Muna so a bar yara 'yan mata su koma makaranta. Ka san idan yarinya ta yi karatu ba za ta yi aure da wuri ba har haihuwa ta yi mata wahala. Za ka ga cewa [macen da ta yi karatu] ta fi kwarewa wurin lura da mijinta da 'ya'yanta. A rika bai wa mace tazara kada yau ta haihu gobe ta haihu."

Da aka tambaye ta shin ba ta ganin yawan al'umma rahama ne, misali irinsu China da India, sai Hajiya Zainab ta ce "yawan jama'a albarka ne amma ya kamata ka san cewa wadannan kasashe da ka ambaci sunansu suna iya ciyar da dukka mutanensu, mutum zai je asibiti ya samu kyakkyawar kula, yaro zai je makaranta ya samu karatu kyauta."

Buhari ya san 'yan Najeriya na shan wahala

Ministar ta amince cewa gwamnatin Shugaba Buhari tana sane cewa 'yan kasar na fama da ku'uba saboda matsin tattalin arziki da kasar ke ciki.

Ta ce sun karbi mulkin Najeriya ne lokacin da kasar ke dab da fadawa masassarar tattalin arziki amma sun yi kokari wajen fitar da ita daga cikin matsi ko da yake ba za a ga hakan ba sai nan gaba.

"Mun san cewa mutane suna cikin wahala kuma ba ma jin dadi. Abin yana batawa shugaban kasa rai amma dole ne a sha wannan magani domin nan gaba a samu koshin lafiya.

Labarai masu alaka