Musulmi na bikin Maulidi a fadin duniya

A taron Maulidin Nyass mutumin ya yi kalaman

A wannan Talatar ce, 12 ga watan Rabiul Awwal, ranar da wani bangaren musulmin duniya ke bikin zagayowar ranar da aka haifi manzon Allah, Annabi Muhammad S.A.W.

Sai dai ba dukkanin Musulmi ne ke bikin ranar ba, saboda sabanin fahimta.

BBC ta tattauna da Sheikh Nur Arzai, wani malamin darikar Tijjaniyya a Kano, dangane da muhimmancin ranar, inda malamin ya ce wannan rana na da matukar muhimmanci.

Sheikh Arzai, ya ce saboda muhimmancin wannan rana, Annabi SAW, ya kan azuminci ranar, sannan kuma ya yi umarni da a rinka yin azumi a ranar Litinin, wanda mafi yawancin mutane kan yi azumi a wannan rana.

Shaihin malamin, ya ce daga cikin abinda ake so duk wanda ke ganin muhimmanci wannan rana ya yi sun hadar da karatun Al-Qur'ani da karatun Hadisan Manzon Allah SWA, ayi zikiri, ayi salatin Annabi SAW, da yabonsa, sannan kuma a fadi ainihin dabi'unsa domin masu sauraro su yi koyi.

Sheikh Arzai, ya ce ya kamata al'ummar musulmai su yi bikin wannan rana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da nuna farin ciki, amma a guji abinda zai kaucewa ka'ida.