Boko Haram 'ta kashe sojojin Najeriya 53'

Shekau Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun kashe soji da manoma 53 a hare-haren da suka kai a kwana uku.

Sai dai rundunar sojin kasar ta yi gum da bakinta game da wadannan rahotanin kashe-kashe.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wasu sojoji na cewa an kashe akalla dakaru 43 a kauyen Metele kusa da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi.

"An murkushe dakarunmu sannan 'yan ta'adda sun kama sansaninmu bayan sun yi ba-ta-kashi,' a cewar sojin.

Ya kara da cewa ana can an bazama cikin dazukan da ke yankin domin neman sojojin da suka bata bayan harin.

Wasu 'yan kato-da-gora sun shaida wa AFP cewa mayakan na Boko Haram sun isa kauyen ne cikin motoci kusan 20 kuma ba a samu dauki daga wurin karin sojoji ba sai bayan "sun mamaye sansanin sannan sun kwashe makamai."

A ranar ce kuma 'yan Boko Haram suka kai hari a kauyen Gajiram da asubahi. Kauyen yana da nisan kilomita 80 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Sun kwashe awoyi da dama suna gumurzu, in ji wani mazaunin kauyen a hirarsa da AFP.

Kamfanin dillancin labaran ya ambato wata kungiya da ke sanya ido kan bayanan sirri SITE na cewa wani bangare na kungiyar ta Boko Haram ya dauki alhakin kai hari a kauyukan Metele da Mainok, inda ya yi ikirarin kashe soji 42 baya ga kwashe tankokin yaki hudu da wasu motocin soji

Kazalika, ranar Litinin mayakan Noko Haram sun kai jerin hare-hare inda suka kashe manoma tara sannan suka sace mutum 12 a kauyen Mammanti , a cewar AFP.

Wani mazaunin garin, Usman Kaka, ya shaida wa AFP cewa "mayakan Boko Haram sun z ne a kan kekuna inda suka bude wuta a kan garin."

Wani dan kato-da-gora Muhammad Mammanti ya ce masu tayar da kayar bayan sun halaka mutum uku da suka ki yarda a sace su.

Kungiyar Boko Haram dai ta matsa kaimi wurin kai hare-hare a baya bayan nan, matakin da masu sharhi kan shana;in tsaro ke cewa yunkuri ne na nuna cewa ba a ci karfinsu ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka