Mata 100: Sai na yarda maza ke kara aure

Nenney Shushaidah Hakkin mallakar hoto Joshua Paul for the BBC

Shari'ar Musulunci hanya ce ta gudanar da rayuwar Musulmi gaba daya ko da yake wasu mutane a yammacin duniya na sukar wasu dokokinta.

Sai dai daya daga cikin masu shari'a a babbar kotun Malaysia ta ce aikinta ya ba ta dama ta kare hakkin mata a kasar ta Malaysia wacce akasarin mazaunanta musulmai ne.

A kullum mai shari'a Nenney Shushaidah tana gudanar da shari'a biyar kuma takan saurari kararraki 80 a duk mako.

'Yan kasar Malaysia suna da sassaukan ra'ayin addinin musulunci ko da yake ana kara samun masu tsattsauran ra'ayi da kuma yin amfani da dokoki masu tsauri.

Don haka ne dubban Musulman kasar ke amfani da su a harkokin tarbiya da aure. An bukaci wadanda ba musulmai ba su rika amfani da dokokin da ba ruwansu da shari'a.

Tana yanke hukunci a kan komai kama daga lamarin kudi ga wadanda suka shafi shari'ar Khalwat [musulmai ma'aurata da aka kama su suna abubuwan da bai kamata ba]. ​​

Hakkin mallakar hoto Joshua Paul na BBC
Image caption Malaysia kasa ce da Musulmai sun fi yawa

Amma ta fi gwaninta a kula da yara da kuma batun auren mace sama da daya - abu ne a musulunci da ya ke ba maza ikon iya auren mata hudu, wanda ya halarta a dokar Malaysia.

Mai shari'a Shushaidah ta ce akwai dalilai masu yawa da take dubawa kafin, alal misali, ta bari na miji ya auri fiye da mata daya.

"Kowane lamari daban ne," in ji ta. "Ba za ku iya cewa wai gabaki daya shari'ar musulunci na fifita maza kuma ba ta kula da mata ba... Ina so in gyara wannan kuskure."

Hakkin mallakar hoto Joshua Paul na BBC
Image caption 'Irin wadannan rigunan nawa na tuna mun dumbin nauyin da ke kaina a matsayin Mai shari'a'

Wajibi ne duk wadanda ke cikin auren da akwai mata fiye da daya su kasance suna cikin kotun mai shari'a Shushaidah.

"Ina so in ji daga kowa, ba kawai daga maza ba," inji ta.

"Ina tattaunawa da mata don gano idan sun yarda da shirin. Yana da muhimmancin cewa sun yarda saboda idan na ga wasu alamomi da suka nuna cewa ba sa so, to ba zan ba da izini ba."

"Ni mace ce kuma zan iya fahimtar cewa mafi yawan mata ba za su so kishiya ba. Amma hakan ya halatta a addinin Musulunci, kuma kotunan Malaysiyan sun kafa dokoki masu girma don gudanar da hakan."

"Dole namiji ya zo da dalilai mau karfi idan yana neman karin aure," in ji ta.

"Dole sai ya nuna cewa zai iya kula da hakkokin matarsa ​​ta farko da kuma matan da za su zo daga baya. Kuma ba a yarda ya ki kula da kowace daga cikinsu ba."

Alkali Shushaidah ta kara da cewa wasu matan suna iya goyon bayan ra'ayin.

Ta tuna wani misali wanda ya shafi wata wadda take cikin mummunar rashin lafiya wadda ba ta iya kara haihuwa.

"Tana kaunar mijinta kuma ta so in ba shi izinin sake aure, sai na ba da izini."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu suka da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suna jayayya kan cewa ana amfani da Shari'a don nuna bambanci

Mece ce Shari'a?

  • Shari'a ita ce tsarin shari'a ta musulunci, wanda aka samo daga Al-Kur'ani mai girma; da Hadisi, maganganu da halayen Annabi Muhammad S.A.W; da kuma hukunce-hukuncen malaman Musulunci.
  • A Malaysia, ana amfani da su a wurare daban-daban a jihohin kasar.
  • Tana kare kimar addininta saboda dokokin da ke kunshe da shi ta hanyar tabbatar da cewa akwai adalci a ciki.
  • Amma masu suka da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suna jayayyar cewa ana amfani da Sharia ta hanyar da ba ta dace ba.

Mataimakin Darakta na hukumar kare hakkin bil Adama ta Asia Human Rights Watch, Phil Robertson ya shaida wa shirin Mata 100 na BBC cewa: "Ba ma adawa da Shari'a da ba ta nuna babanci a kan mata da masu luwadi ko tsiraru marasa ringaye a bangaren addini da zamantakewa."

"Amma matsalar dokar Shari'a a Malaysia ita ce sau da yawa takan aikata haka.

"Addini ba karbabben dalilin ba ne na karya ka'idodin kare hakkin dan Adam na kasashen duniya na daidaito da rashin nuna bambanci."

Alal misali, masu fafutukar kare hakkin dan Adam ba su ji dadin bulalar da aka yi wa wadansu mata biyu 'yan Malaysia da aka kama da laifin niyyar yin madigo ba, sun ce ba a yi amfani da Sharia yadda ya kamata ba.

Mai shari'a Shushaidah ta ce ba za ta yi magana a kan al'amarin ba, amma ta ce: "Yin bulala a karkashin Shari'a yana ba da horo ga masu laifi don kada su sake maimaita irin aikin."

Mai shari'a Shushaidah kuma ta ce ba kullum ba ne Shari'a ke goyon bayan maza ba.

"An kafa dokarmu ne domin kare hakkokin mata. Yana kula da jin dadinsu da kiyaye rayuwarsu," inji ta.

"Musulunci yana daukaka mata, saboda haka, a matsayinmu na mata, dole ne mu koma ga koyarwarsa kuma mu tabbatar da muna amfani da Shari'a yadda ya kamata."

Babban abin da ya fi damunta shi ne musulmai maza da ke kin bin Shari'a ta hanyar yin aure a kasashen waje.

"Dokar Malaysia ba za ta hau shi ba idan ya yi aure a kasashen waje. Wasu mata suna yarda da wannan don kare mazajensu amma ba su fahimci yadda hakan ke yi masu illa ba, "in ji ta.

"An kafa shari'armu ne domin kare hakkokin mata da kuma tabbatar da cewa sun yi wa matansu adalci."

Kungiyoyin mata kamar Sisters in Islam sun nuna "rashin wakilcin mata" a kotu da kuma "yadda maza ke mamaye komai" a cikin tsarin.

"Yanayin shari'a a Malaysia ba wai kawai nuna bambanci ga mata yake ba, yana nuna mata a matsayin masu janyo matsaloli a cikin al'ummar," in ji kakakin kungiyar Majidah Hashim.

"Cibiyoyin Muslunci na kasar... ba su yi kokari ba don tabbatar da ana yi wa mata adalci.

"A gaskiya ma, da 'yan kwanan nan, kararrakin da aka shigar na mata a karkashin Shari'a sun nuna cewa ana hana su magana kuma ana hana su samun adalcin da ya kamata.

Hakkin mallakar hoto Joshua Paul for the BBC
Image caption Nenney Shushaidah

Wannan ya sa zaben Mai shari'a Shushaidah abu mai matukar muhimmanci.

"A da, mafi yawan alkalan Shari'a sun kasance duk maza ne wadanda suke cewa ba su ga amfanin mata su zama alkalai ba," in ji Shushaidah.

"Ban taba tunanin zan iya zama Mai shari'a ba," in ji ta.

"A matsayin lauya, ban taba sanin cewa ba ko zan iya daukar nauyin babban mukami irin haka ba da ke magance matsaloli masu rikitarwa. Kuma a matsayin mace, na ji shakku da tsoro."

"Wani lokaci ba na jin dadi sosai. A matsayina ta mace, dole ne in ji haka, kuma zan yi karya idan na ce ba na jin komai.

"Amma ni mai shari'a ce kuma dole in tabbatar da cewa ina da adalci. Saboda haka, wajen yanke shawara, ina yin kokarin yin hakan. Ina amfani da mafi kyawun shaida da na samu a kotu."

Mene ne Shirin Mata 100 na BBC?

BBC 100 Women na zabar sunayen mata 100 sannanu masu tasiri a sassa daban-daban na duniya kowace shekara, sai kuma a ba da labarinsu.

Wannen shekarar ta yi tasiri sosai a kan kare hakkokin mata a duniya, Saboda haka a 2018 Shirin Mata 100 na BBC zai haska rayuwar matan da suka shige gaba wajen amfani da hamasa da hazaka da fushinsu wajen kawo sauyi a tsakanin al'ummominsu.

Za ku iya samun mu a shafinmu na Facebook da Instagram da na Twitter da hanyar amfani da mau'du'in #100Women

Labarai masu alaka