Sojoji sun ceto daliba da aka sace a Kamaru

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yankin Ambazoniya da ke magana da turancin Ingilishi yana fuskantar tashe-tashen hankula

Jami'an tsaro a Kamaru sun ce sun ceto wasu dalibai tara na wata makarantar sakandare a birnin Kumba, da shugaban makarantar, wadanda ake zargin masu fafutuka na Ambazoniya suka sace ranar Talata.

A musayar wuta tsakanin jami'an da 'yan tawaye, an kashe masu fafutikar guda shida, sannan an kuma karbe makamai hudu da wasu harshasai.

Maharan sun kutsa cikin makarantar ne suka yi awon gaba da daliban da malaminsu.

An kubutar da daliban gaba dayansu da shugaban makarantar ba tare da sun jikkata ba.

Tun da yammacin Talatar ne jami'an tsaro suka kubutar da uku daga daliban bayan musayar wuta tsakanin su da wadanda suka sace daliban.

Farmakin da jami'an suka kai ya biyo bayan binciken da suka gudanar sakamakon sace daliban a yankin masu magana da turancin Ingilishi.

Wannan ne karo na biyu da ake sace dalibai a yankin na Ambazoniya a cikin watan nan.

A farkon watan an sace dalibai 81 a wata makarantar sakandare a yankin, kafin daga baya jami'an tsaro sun kubutar da su kwanaki kadan bayan sace su.

Yankin Ambazoniya da ke magana da turancin Ingilishi yana fuskantar tashe-tashen hankula tsakanin masu fafutukar aware na yankin, da kuma jami'an tsaron gwamnati da ke yunkurin murkushe su.

Suna son samar da kasa mai cin gashin kanta da suka ba sunan Ambazonia.

Kamaru - har yanzu kawuna basu hadu ba

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Turawan mulkin mallaka ne suka "tsaga" nahiyar Afirka zuwa kasashe domin amfaninsu
  • Jamus ta mulki Kamaru a shekarar 1884
  • Sojojin Birtaniya da Faransa sun fatattaki Jamusawa a 1916
  • Bayan shekara uku an raba Kamaru gida biyu - kashi 80 cikin 100 na Faransa, kashi 20 cikin 100 kuma na Birtaniya
  • Yankin da ke karkashin ikon Faransa ya sami 'yanci a 1960
  • Bayan zaben raba gardama, yankin Kudancin Kamaru ya hade da Kamaru, inda yankin Arewacin Kamaru ya hade da Najeriya mai amfani da harshen Ingilishi.

Labarai masu alaka