Ana alhinin mutuwar mawaki Mamman Barka na Nijar

Barka Hakkin mallakar hoto Mammam Barka
Image caption Shahararren mawakin ya bar mata daya da 'ya'ya 10

A ranar Laraba da safe ne Allah Ya yi wa sanannen mawakin nan na Jamhuriyar Nijar, Mammam Barka rasuwa a Yamai babban birnin kasar.

An haife shi a shekarar 1959, ya kuma yi fice wajen yin wakokin gargajiya inda har aka san shi a duniya.

Tuni dai dimbin mutane a jamhuriyar Nijar suka fara bayyana jimaminsu bayan mutuwarsa.

Mai shekara 60 da haihuwa, shahararren mawakin ya bar mata daya da 'ya'ya 10 - mata biyar, sai kuma maza biyar.

Ya fara sana'ar wakarsa ta hanyar amfani da gurumi.

Amma a shekarar 2002, sai ya sauya hanya saboda samun daukar nauyin karatu da ya samu daga Hukumar UNESCO

Ya yi amfani da kudin don sake farfado da kida ta amfani da abin kida na biram, wanda mutanen Boudouma suke amfani da shi - wato masunta a wajen yankin Tafkin Lake.

Ya hadu da wanda ya fi kowa iya amfani da biram, Boukar Tar, wanda ya koya masa yadda ake amfani da nau'in, wanda aka yarda yana kare ruhun tafkin.

Barka ya sa irin wannan kida ya yi tashe "inda ya ja hankalin duniya a kan yadda yake amfani da kayan kidan da ya harhada", a cewar Soas a shekarar 2009.

Ana sa ran za a binne marigayin a garin Tesker a ranar Alhamis.

An san shi da rera wakokinsa a harshen Hausa da Faransanci.

Wannan ita ce daya daga cikin wakokinsa na farko, Ameram - inda yake yabon kirkin wata mata da ya taba haduwa da ita lokacin da yake malami- aikinsa na farko.

Barka ya kuma kasance marubucin littattafai uku a kan al'adun Nijar.

A karshen rayuwarsa ya koya wa mutane yadda ake amfani da garaya.

Image caption Mammam Barka

Labarai masu alaka