Wata mata ta kashe saurayinta ta yi abinci da namansa

A traditional Emirati dish called chicken machboos Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Matar ta yi wani nau'in abinci irin wannan da naman saurayin nata ta bai wa wasu suka ci

Masu shigar da kara sun ce ana zargin wata mata 'yar kasar Moroko da kashe saurayinta sannan ta yi abinci da namansa ta bai wa wasu ma'aikata 'yan Pakistan a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Matar ta kashe saurayin nata ne wata uku da suka gabata, amma sun ce sai a kwanan nan ne aka gano abun da ya faru bayan da aka ga hakorin mutum a cikin injin markadenta.

Jaridar kasar mai suna The National ta ruwaito matar na cewa ta amsa laifinta amma kuma tana "ta samu tabin hankali ne a wannan lokacin."

Za a fara yi wa matar, mai shekara 30 shari'a kafin a kammala bincike.

Ta shafe shekara bakwai tana hulda da saurayin nata.

Jaridar The National ta ce ta kashe shi ne bayan da ya shaida mata cewa yana shirin auren wata budurwar daga Moroko.

A yayin da 'yan sanda ba su yi bayanin yadda aka kashe shi ba, sun ce budurwar tasa ta yi wani abincin gargajiya na kasarsu da naman jikinsa ta kuma raba wa wasu ma'aikata 'yan Pakistan da suke kusa da gidanta.

An gano lamarin ne kawai bayan da dan uwan mamacin ya je nemansa a gidan matar da ke birnin Al Ain wanda ke kan iyakar UAE da Oman.

Jaridar ta ce a can ne ya gano hakorin mutum a cikin injin markade.

Daga nan sai mutumin ya je ya shaida wa 'yan sanda batun batan dan uwansa, su kuma suka yi gwajin kwayoyin halitta a hakorin suka kuma gano cewa na saurayin nata ne.

A cewar 'yan sanda, matar ta fara shaida wa dan uwan saurayin nata cewa ta kore shi ne daga gidan.

Amma kafar yada labarai ta Gulf mai cibiya a Dubai ta ce daga bisani matar ta yi lakwas ta kuma dauki alhakin kashe shi bayan da 'yan sanda suka tuhume ta.

An ruwaito ta sau da dama tana cewa ta nemi taimakon kawarta ne ta gyara gidan nata bayan da ta aiwatar da kisan.

An dai tura ta asibiti don a yi mata gwajin kwakwalwa.

Labarai masu alaka