Ango ya je daurin aurensa da harsashi a jikinsa

Ango da abokansa Hakkin mallakar hoto MONEY SHARMA/AFP/GETTY

'Yan sanda a kasar Indiya sun ce, wani ango ya sha rantsuwar aure duk da harbinsa da aka yi a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa inda za a daura aurensa a birnin Delhi na kasar.

Bayan harbin da wasu 'yan bindiga suka yi wa ango, an yi maza an garzaya da shi asibiti, amma sa'oi bayan an duba lafiyarsa ya ce a kai shi wajen daurin aurensa domin a kammala daurin auren, duk kuwa da kasancewar ba a cire harsashin da aka harbe shi ba a kafada.

Yanzu haka 'yan sanda sun bazama neman wasu mutum biyu da ake zargi.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da irin haka ta faru wato a bude wuta ko harbi a wajen taron daurin aure.

A shekarar watan Aprilun da ya wuce, an kashe wasu angwaye a lokacin bikinsu, sannan kuma a shekarar 2016 ma an kashe wasu angwayen.

'Yan sanda sun ce an harbi angon ne a lokacin da ya ke tare da rakiyar abokansa suna tafiya ana cashewa domin zuwa inda za a daura auren.

Likitoci dai sun tsayar da jinin da ke zuba daga jikin angon sakamakon harbin, amma kuma ba su kai ga cire harsashin ba saboda sai an yi babbar tiyata angon ya matsa zai tafi a daura aurensa.

Bayan kammala daura auren ne sai angon ya koma asibiti domin a cire masa harsashin.

Labarai masu alaka