Har yanzu Jonathan na boye-boye kan sace 'yan matan Chibok —Shettima

Goodluck Jonathan da Kashim Shatima Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabannin biyu suna zargin juna kan batun sace 'yan matan Chibok

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce sakacin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi ne ya janyo aka kasa ceto 'yan matan Chibok jim kadan bayan sace su a 2014.

Gwamna Shatima na mayar da martani ne kan zargin da Goodluck ya yi cewa sace 'yan matan laifin gwamnatin Borno ne.

A littafin wanda aka kaddamar a Abuja ranar Talata mai suna "My Transition Hour", Jonathan ya ce da gangan gwamnatin Borno ta ki amincewa da shawarar gwamnatin tarayya cewa a kwashe 'yan matan daga makarantar gabanin jarrabawa.

Mista Jonthan ya kuma yi zargin cewa jam'iyyar APC da gwamnatin Bornon sun yi amfani da batun sace 'yan matan na Chibok wajen cimma manufar siyasa.

Sai dai a martanin da gwamnan na Borno Kashim Shettima ya mayar wa tsohon shugaban, ya ce da gangan gwanatin tarayya a lokacin ta ki amincewa an sace yaran da farko, wanda hakan ya kawo tsaiko wajen yunkurin ceto su.

Gwamna Shettima ya ce ya yi mamakin yadda a cikin littafin tsohon shugaban kasar ya ki bayyana sakamakon binciken kwamitin da shi Jonathan ya kafa, wanda aka mika masa ranar 20 ga watan Yuli 2014 kunshe da bayanai dalla-dalla kan ganawar da manyan jami'an tsaron kasar suka yi da iyaye da 'yan matan da suka tsira da malaman makarantar da kuma jami'an shirya jarrabawar kammala sikandare WAEC.

Gwamnan ya ce a bayyane take Jonathan ya boye sakamakon binciken, domin ya boye gazawar gwamnatinsa kan kasa ceto 'yan matan da kuma magance matsalar Boko Haram.

Shettima ya ce bayan karanta littafin tsohon shugaban, ya gamsu cewa Jonathan yana da karancin fahimtar al'amura a gwamnatinsa.

Sai dai har kawo yanzu bangaren na tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan bai mayar da martani kan zarge-zargen gwamnan na jihar Borno ba.

Littafin da tsohon shugaban ya buga ya mayar da hankali ne kan abubuwan da suka faru dab da zai bar mulki, da kuma wasu manyan batutuwa da suka taka rawa a yakin neman zabe.