Na fi Buhari yaki da cin hanci da rashawa — Jonathan

Buhari da Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Goodluck Jonathan ne ya mika wa Buhari mulki a watan Mayun 2015

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya soki yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa gwamnatin Buhari ta fi mayar da hankali ne kawai wajen farfaganda a kafafen watsa labarai.

Goodluck ya yi zargin cewa ya mikawa gwamnatin Buhari tattalin arziki ingantacce da kimarsa ta kai sama da dala biliyan 500, amma da zuwan Buhari ya jefa kasar cikin koma-bayan tattalin arziki, ta hanyar bata wa kasar suna, sannan kuma ya ke zargin gwamnatin ta Goodluck kan duk wata matsala da gwamnatin mai ci ta haifar wa kanta.

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a cikin littafinsa my suna "My Transition Hours" wanda aka kaddamar a Abuja ranar Talata.

Sai dai har kawo yanzu gwamnatin ta Buhari ba ta mayar da martani kan zarge-zargen na Jonathan ba.

Jonathan ya ce gwamnatin Buhari ta dukufa wajen shafe duk wani abin kirki da gwamnatinsa ta yi, ta hanyar zargin cewa gwamnatin PDP ta wawashe dukiyar kasa.

Ya ce gwamnatinsa ta yi yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya fiye da duk wata gwamnati da aka taba yi a kasar.

"Sannan yawan mutanen da aka kama aka kuma yanke musu hukunci kan rashawa da cin hanci ya zarta na duk wata gwamnati da aka taba yi a tarihin Najeriya," a cewar Jonathan.

Tsohon shugaban ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin bambance tsakanin sata da rashawa, domin tantance tsakanin laifukan biyu da suka banbanta wajen hukunci.

Ya zayyana wasu matakai da gwamnatinsa ta dauka da suka hada da fito da tsarin Asusun Kasa Bai Daya (TSA), da lambar banki ta bai daya BVN, da kuma tantance ma'aikata ta na'ura, wanda ya sa gwamnati ta samu rarar sama da Naira biliyan 100 da ake biyan albashi ga ma'aikata da kuma 'yan fansho na bogi.

Ya ce 'yan Najeriya sun goyi bayan Buhari ne saboda yaki da cin hanci da rashawa, to amma sun dawo daga rakiyar gwamnatin saboda yadda jami'an gwamnatin ke bata wa Najeriya suna ta hanyar bayyana 'yan kasar a matsayin wadanda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu.

Jonatha ya ce babban aikin shugaban kasa shi ne ya kwarzanta kasarsa a idon duniya, ya ce sai dai abin takaici, yadda kafofin watsa labarai ke bayar da rahotannin kalaman Buhairn kan cin hanci da rashawa ya yi wa kasar mummunar illa.

Hakkin mallakar hoto Jonathan
Image caption Jonathan ya ce Buhari yana batawa Najeriya suna a idon duniya

Ya ce ba don kare martabar ofishin shugaban kasa da ya taba rikewa ba, da ya bankada irin cin hanci da rashawar da wasu manyan jami'an gwamnatin Buhari suka tafka, wadanda kuma sune kan gaba a kwarmaton yaki da cin hanci da rashawa.

Tsohon shugaban ya ce zai yi wuya a kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya matukar ba a sauya tsarin amfani a siyasar kasar ba, wanda zai yi wahala mutum ya sanya kudin halaliya da ya sha wahala wajen samun.

Littafin na Jonathan dai ya fara janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

Ko a ranar Laraba ma sai da gwamnan jihar Borno Kashim Shatima ya mayar wa shugaban kasar martani kan batun sace 'yan matan Chibok a shekarar 2014.

Littafin na Jonathan dai mai suna "My Transition Hours" ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman batutuwa da suka faru a 'yan watannin karshe na mulkin shugaba Jonathan.

Sai dai kuma ya tabo wasu batutuwan da suka hada da batun cire tallafin man fetur.

Hakkin mallakar hoto Jonathan
Image caption Wannan ne karon farko da Jonathan ya yi magana kan gwamnatin sa tun bayan barin gwamnati

Labarai masu alaka