Goodluck Jonathan: 'Ana yada jabun littafina a intanet'

jonathan Hakkin mallakar hoto Jonathan Twitter

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ankarar da mutane cewa an fara yada jabun sabon littafinsa a intanet mai suna "My Transition Hours'', wanda ya kaddamar a ranar Talata.

Ya kaddamar da littafin ne a wani bangare na bikin cikarsa shekara 61 da haihuwa.

A wasu sakonni da ya wallafa a shafukansa na Facebook da Twitter ranar Alhamis, Mista Jonathan ya ce: "An sanar da mu cewa wasu masu yi mana bi ta da kulli suna ta yada littafin boge da cewa shi ne wanda muka kaddamar a kwanan nan.

"A don haka muna shawartar mutane da su guji wannan littafi da ake wallafawa ko rarraba shi ta intanet, don an kage shi ne kawai domin a yaudari al'umma."

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa: "Kuma ku gane cewa littafina nai taken #MyTransitionHours, ba a fara sayar da shi a intanet ba, don haka wanda ake yada wa a intanet na karya ne don a rudi mutane.

"Don haka muna shawartar jama'a su yi watsi da wancan din don abin da ke kunshe ciki ba iri daya ne da wanda na kaddamar ba kwana biyu da suka gabata a Abuja."

Mista Jonathan ya wallafa yadda abin da littafin ya kunsa na gaskiyar da na jabun a Twitter don a bambance, kamar yadda ku ke gani a sama.

A cikin littafin akwai inda tsohon shugaban Najeriyar ya soki yadda Shugaba Muhammadu Buhari yake yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa gwamnatin Buhari ta fi mayar da hankali ne kawai wajen farfaganda a kafafen yada labarai.

Sannan ko a ranar Laraba ma sai da gwamnan jihar Borno Kashim Shatima ya mayar wa tsohon shugaban kasar martani kan batun sace 'yan matan Chibok wanda ya faru a shekarar 2014.

A littafin na "My Transition Hour", Jonathan ya ce da gangan gwamnatin jihar Borno ta ki aiki da shawarar gwamnatin tarayya cewa a kwashe 'yan matan daga makarantar gabanin jarrabawa.

Sai dai kuma har a bayanin da Jonathan ya yi a Twitter bai ce ko wadannan batutuwa biyu suna cikin abin da littafin nasa na ainihi ya kunsa ko a cikin jabun suke ba.

Littafin dai na Jonathan yana ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

Littafin ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman batutuwa da suka faru a 'yan watannin karshe na mulkin Shugaba Jonathan.

Sai dai kuma ya tabo wasu batutuwan da suka hada da batun cire tallafin man fetur da sauransu.