Adel al-Jubeir: 'Ba zai yiwu a cire Yariman Saudiyya ba'

Adel al-Jubeir Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir ya ce kiraye-kirayen cire Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman "wata iyaka ce da ba za'a iya ketarata ba," yayin da kasar take fuskantar matsin lambar bayan kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Adel al-Jubeir ya ce ba da sanin yariman aka kashe dan jaridan a ranar 2 ga watan Oktoban a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul a kasar Turkiyya.

Wannan yana zuwa ne kwana daya bayan majalisar dokokin Amurka ta bukaci bincike kan ko yariman yana da hannu a kisan dan jaridan.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce "wata kila da sanin yariman aka kashe Khashoggi" kuma ya ce wata kila "babu sanin yariman a kisan dan jaridan."

Adel al-Jubeir ya ce: "a Saudiyya shugabancin wata iyaka ce da ba a ketara ta ba. Sarki (Salman) da kuma Yarima mai jiran gado (Mohammed bin Salman) wasu iyakoki ne da ba za a iya ketara su ba."

A ranar Asabar ne dai kafofin yada labaran Amurka suka ruwaito cewa hukumar leken asirin Amurka ta ce bincikenta ya tabbatar da Yariman mai jiran gado Saudiyya Muhammad bin Salman ne ya bayar da umurnin kisan Mista Khashoggi.

Sai dai kuma da yake bayani game da rahoton, shugaba Trump ya jaddada muhimmacin dangantar da ke tsakanin kasarsa ta Amurka da Saudiyya, yana mai cewa Amurka na da kyakkyawar alaka da Saudiyya.

"Sun bamu ayyuka da kasuwanci da yawa da kuma bunkasa tattalin arzikinmu, sun kasance aminan gaskiya ta fuskar samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arzikinmu, kuma a matsayi na shugaban kasa dole sai na tattauna da CIA"

Gwamnatin Saudiyya dai ta musanta zargin, kuma tuni Amurka ta ce akwai alamar tambayoyi da dama a kan batun kashe dan jaridar na Saudiyya Jamal Kashoggi a watan jiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amurka ta ce za ta tabbatar da ganin wadanda ke da hannu a kisan sun fuskanci hukunci duk da kara jaddada amincinta da Saudiyya.

Shugaba Trump na dada fuskantar matsin lamba game da al'amarin kisan na khashoggi.

Wasu manyan 'yan siyasa a Amurka sun bukaci a gaggauta daukar mataki tun kafin Yariman Saudiyya da ake zargi ya gaggauta kashe mutanen da suka aiwatar da umarnin da ya ba su.

Labarai masu alaka