Shugaba Buhari ya mayar wa Goodluck Jonathan martani

Buhari da Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar wa tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan martani game da yadda ya ce an samu karuwar cin hanci da rashawa a kasar a halin yanzu idan aka kwatanta da tsohuwar gwamnatinsa.

Wata sanarwar da kakakin Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya aike wa BBC, ta musanta ikirarin tsohon shugaban.

Mista Goodluck Jonathan ya yi ikirarin hakan ne a wani sabon littafi da ya kaddamar a ranar Talata.

"Shugaba Buhari ya kafa tarihi a fannoni biyu. Na farko shi ne yadda gwamnatinsa ta tabbatar da bangaren shari'a na bin ka'idojin aikinsa, wanda ya hada da hukunta alkalai," in ji Garba Shehu.

Ya ce shugaban ne "na farko" da ya taba yin haka a tarihin kasar.

Har ila yau, ya ce wannan ne karo na farko da aka gurfanar da manyan hafsoshin sojojin kasar a gaban kotu saboda zargi aikata laifukan da suka jibanci cin hanci da rashawa.

"Wannan ne karon farko da jam'iyya mai mulkin kasar ta gurfanar da wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada da tsofaffin gwamnonin jihohi wadanda 'yan jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne," in ji mai magana da yawun Shugaba Buharin.

Sanarwar ta lissafta wasu matakai da kudurin dokoki da kuma gyare-gyare ga wasu dokokin kasar domin inganta yakin da take yi da masu cin haci da laifukan da ke gurgunta tattalin arzikin kasar.

A karshe sanarwar ta ce a lokacin da gwamnatin Buhari ta karbi mulki a watan Mayun 2015, asusun ajiyar hukumar EFCC na da naira biliyan 19.5 ne, kamar yadda wani rahoto na ofishin ministan shari'a ya bayyana.

Amma bayan shekara daya da fara aiwatar da yaki da "cin hanci da rashawa da wannan gwamnatin ke yi, an samu karuwar kudade a cikin asusun zuwa naira biliyan 279".