An kashe yaro saboda ya ki yin 'aikin makaranta'

'Yan sanda Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata majiya da ga rundunar 'yan sanda a kasar Faransa, ta ce an kama wasu iyalai hudu da ake zargin sun kashe wani yaro dan shekara tara har lahira saboda bai yi aikin jinga wato home work ba.

Wannan lamari dai ya faru ne a birnin Mulhouse da ke gabashin kasar Faransa.

'Yan sanda sun ce, an yi wa yaron dukan tsiya ne da tsintsiya, inda a wajen kuma akwai babban wansa da yayinsa mata biyu.

Koda ya ke a lokacin da aka daki yaron, mahaifiyarsa ba ta gida amma ta san abinda ke faruwa a gida don haka ne itama aka kamata.

Al'amarin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta wuce.

Za dai a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika gaban shari'a, inda za a bukaci jin ainihin abinda ya faru.

An dai fi zargin yayan yaron wanda ke da shekara 19 da haihuwa da sanadiyyar mutuwar yaron sakamakon dukan ya yi masa tsintsiya.

A cikin wani rahoton binciken musabbabin mutuwar yaron da aka gudanar a asibiti, an gano cewa yaron ya mutu ne saboda bugun zuciya, kuma an ga tsinken tsintsiya a tafin kafar yaron duk ya makale.

Mutuwar yaron ta zo ne adai-dai lokacin da majalaisar wakilan kasar ta Faransa da ke kokarin sanya doka a kan azaftarwar da iyaye ke yi wa 'ya'yansu a kasar.

Labarai masu alaka