An hana sayar da kodin da tramadol a Ghana

Yadda ake kwankwadar kodin

Ma`aikatar lafiya a Ghana, ta sanar da hana sarrafawa da kuma rarraba duk wani maganin tari da ke dauke da sinadarin kodin a cikinsa.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce, an kwace rijista tare da janye dukkan izinin gudanar da hada-hadar kodin da kuma bayar da umarni a kan kada wanda ya kara sarrafawa ko shigo da shi ko kuma sayarwa a kasar.

Sanarwar ta kuma ankarar da al`ummar kasar baki daya cewa, daga yanzu sinadirin kodin ya shiga sawun kwayoyin da ake kayyade su, sannan kuma sai idan likita ya rubuta kafin a saya.

Sannan kuma an hana shigowa da sarrafa kwayar tramadol ko kuma sayar da ita, don haka hukumar tantance abinci da magunguna ta kasar ce za ta rinka kayyade adadi da karfin kwayar tramadol.

Ghana ta bi sawun Najeriya, wadda a watannin baya ta haramta amfani da kodin bayan wani shirin BBC na Africa eye ya bankado wata badakala a kan sinadarin na kodin.

Maganin kodin da illolinsa

  • Kodin magani ne da ke rage zafin ciwo ko na jiki amma yana cikin magungunan da ke sa ma
  • Idan aka sha shi fiye da kima, to yana janyo tabin hankali kuma yana yin illa ga koda ko hanta ko zuciyar mutum
  • An fi hada maganin tari na kodin da lemun kwalba kuma dalibai ne suka fi shansa.

Daga kasashen waje ne ake shigowa da kodin, amma a cikin Najeriya ne kamfanoni fiye da 20 suke hada magani

  • Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar na kokarin kawarda da matsalar.
  • A samamen da taka kai a baya-baya nan, ta kwato kwalaben Kodin 24,000 daga cikin wata babbar mota a jihar Katsina.

Ta'ammali da kodin babbar matsala ce a Afirka, inda ake samun rahotanni game da wadanda ba su iya rabuwa da shi a Kenya da Ghana da Niger da kuma Chadi

  • A shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta hana amfani da shi a kasar sakamakon rahoton da ta samu game da yawan masu ta'ammali da shi a matsayin kayan mayeye.