'Babu ruwan bil'adama da gushewar manyan halittu'

Tun shekaru miliyan 4.5 da suka wuce dabobbi irinsu dorina ruwa ke fuskantar barazanar karewa Hakkin mallakar hoto MICHAEL LONG/SCIENCE PHOTO LIBRARY
Image caption Tun shekaru miliyan 4.5 da suka wuce dabobbi irinsu dorina ruwa ke fuskantar barazanar karewa

Wani sabon bincike da aka yi ya kawar da fahimtar da aka dauka da dadewa cewa mutanen farko sun taimaka wajen kawar da manyan halittu masu shayarwa daga doron-kasa, wadanda a da suke rayuwa a nahiyar Afrika.

A wannan zamanin akwai nau'ikan manyan dabobbi masu shayarwa, amma a milyoyin shekaru da suka gabata akwai ire-irensu da dama da suke cin tsirai.

Binciken ya ce duk da cewa ba a san dalilin bacewar wadanan dabobbin ba, kwararu na daura alhakin bacewar nau'ikan dabobbin a kan kakaninmu da suka yi amfani da kayayyakin farauta iri na da, suna kashe dabobbi domin su ci.

A yanzu masu binciken, sun ce wadanan nau'ikan dabobbi sun bace a doron kasa tun kafin bayyanar mutum.

Wata makala da aka wallafa a mujallar kimiya ta Tyler Faith, ta ce sauye-sauyen muhalli su suka haifar da gushewar dabobbin daga doron-kasa.

Duk da irin litatafai ko rubuce-rubuce da aka yi shekara da shekaru da ke jadada cewa mutanen farko sun rinka farauta a kan irin wadanan dabobbi a nahiyar Afrika da Asia, har yanzu ba a yi wani binciken a zo a gani ba domin tabbatar da wanna matsayi, a cewar binciken.

A wannan zamanin abin da ake dasu da suka rage a irin wadanan dabobbi sune giwaye da rakumin dawa da dorina ruwa da karkanda.

Sakamon bincike da aka yi, ya nuna cewa shekaru miliyan 7 da suka gabata, akwai nau'ikan irin wadanan dabobbi 28 sun bace daga doron kasa a nahiyar Afrika.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rakumin dawa na cikin dabobbi da ke karewa tun shekara dubu dari 700 da suka wuce

Haka kuma, fara bacewar wadanan dabobbi ta fara ne kusan a shekara miliyan hudu da rabi, da suka wuce, kuma yanayin bacewar ta su bai sauya ba duk da bayyanar halitar mutum irin na wannan zamanin, da ake ganin za ta iya taimakawa wajen bacewar dabobbi a lokacin.

Labarai masu alaka