Gawa ta ki rami a Habasha

Hirpa Negro
Image caption Hirpha Negro

Mazauna wani kauye a Habasha na farin ciki game da farfadowar wani mutum da aka dauka ya mutu.

An ce Hirpha Negero, mai yara biyar ya mutu ne a ranar Talata da misalin karfe goma da rabi na safe.

Sai da aka yi harbin bindiga sau biyu domin a sanar da mazauna kauyen Sibu Sire da ke yankin Oromia da mutuwarsa.

Bayan sa'a daya da mutawar magariyin, sai wanda ke yi wa gawa wanka a kauyen Etana Kena ya sanya Mista Hirpha a cikin akwatin gawar domin a binne shi

Sai dai yayin da aka soma shirye-shiryen binne gawar da misalin karfe uku da rabi na rana, sai masu zaman makoki suka fara jin kara daga cikin akwatin gawar.

"Mutane sun dimauce sai suka fara gudu, kuma babu wani da ya tsaya domin ya taimaka," in ji Mista Etana lokacin da yake bayani game da cewa bayan ya bude akwatin gawar Mista Hirpha ya bukaci a taimaka ma sa.

Mutumin da aka saka a cikin akwatin gawar bayan da aka dauka cewar ya mutu ya shaidawa BBC cewa ya rika jin kukan wani lokacin da yake cikin akwatin. "Numfashi na ya rika dauke wa saboda bana samun iska kuma na rika kokarin cire kyallen da aka saka man, Na galaibata, na kasa fita," in ji shi.

Daga nan ya fara neman dauki yana cewa "shin ko akwai wani kusa?"

Bayan rudanin da aka shiga, sai taron binne gawar ya koma na bikin murna.

Mista Etana wanda kawun Mr Hirpha din ne ya ce, "Na binne mutum iye da 50 ko 60, ban taba ganin a'lamari irin wannan ba, ya yi kama da mutumin da ya mutu."

Dakta Birra Leggese wanda likita ne ya shaidawa BBC cewa Mr Hirpha ya yi 'doguwar suma ne'.

Labarai masu alaka