Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da harin Metele.

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram na ci gaba da zama barazana a Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar cewa an kai wa sansanin sojinta da ke garin Metele a jihar Borno hari.

Ta ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Ta kuma ce tana da ka'idojin fitar bayyanai kan sojojinta da suka rasa rayukansu, kuma sai bayan ta sanar da iyalinsu ne ta ke fitar da sanarwar a kan duk wani abu da ya faru game da sojojinta.

Amma kuma ba ta bayyana adadin sojojin da aka kashe ba, kuma ba tare da yin karin bayani game da harin ba.

Sannan ta musanta rahotannin farko na wasu kafofin watsa labarai da suka hada da na shafukan intanet game da yawan sojojinta da aka kashe a harin.

Ta karyata wani hoton bidiyon da ta kira tsoho ne kan harin da aka kai kan sojojinta, inda ta kira bidiyon a matsayin farfaganda.

Ta kuma ce karin sojojin da aka tura zuwa garin sun shawo kan lamarin kuma al'amurra sun daidaita yanzu haka.

Sai dai bayan kusan mako guda ne da aukuwar lamarin ne rundunar kasar ta fitar da sanarwar kuma wannnan na zuwa ne bayan da Kungiyar ISWA wadda wani bangare na kungiyar Boko Haram da ya balle ta wallafa wani bidiyo inda ta yi ikirarin kai harin.

Akwai rahotannin da ke cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tura ministan tsaron kasar Birgediya janarar Mansur Dan Ali zuwa makwabciyar kasar Chadi domin ya gana da shugaba Idris Deby kan tabarbarewar tsaro a kan iyakar kasashen biyu.

Labarai masu alaka