'Yan sanda sun kame 'yan IPOB 34

'Yan IPOB sun yi kiran a kauracewa zaben 2019 a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan IPOB sun yi kiran a kauracewa zaben 2019 a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama 'yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra su 34 bayan sun kai wa jami'anta hari tare da kashe jami'i daya.

SP Haruna Mohammed, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Babu dai tabbas kan asalin abin da ya haddasa rikicin tsakanin 'yan sanda da 'yan IPOB.

Amma a sanarwar 'yan sandan, ta yi ikirarin cewa an kai wa jami'anta hari ne lokacin da suke kokarin hana 'yan IPOB gudanar da zanga-zanga a Nnewi a ranar juma'a.

Kuma ta ce an kashe dan sanda guda da raunata DPO tare da kone motocinsu na sintiri.

Wasu mazauna yankin sun ce 'yan OPOB sun fito ne suna zanga-zanga a Nnewi suna yin kira ga mutanen gari su kauracewa yin zaben da ke tafe kafin daga bisani su fara arangama da 'yan sanda.

Mazauna garin sun ce akalla mambobin IPOB hudu aka kashe a rikicin.

Sanarwar ta ce an tura 'yan sanda ne zuwa garin Nnewi domin kare jama'ar garin da dukiyoyinsu tare da tabbatar da bin doka da oda.

Ta kara da cewa an tura 'yan sanda ne bayan samun labarin cewa daruruwan 'yan IPOB na shirin tayar da rikici a Nnewi.

"Da zuwan 'yan sanda wurin, 'yan IPOB suka kai ma su hari da adda da jifa da duwatsu, suka cinna wa mota wuta," in ji sanarwar. Ta kara da cewa 'yan IPOB na ta yayata cewa "Ba za a yi zabe ba sai an yi kuri'ar raba gardama."

Barazanar tsaro dai na ci gaba da karuwa a Najeriya inda wannan rikicin ke zuwa a yayin da rundunar sojin kasar ta tabbatar da harin da aka kai wa jami'anta a jihar Borno.

Rahotanni sun ce sama da sojojin Najeriya kusan 100 aka kashe a harin, yayin da dama suka bace.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam irinsu Amnesty International sun zargi jami'an tsaron Najeriya da yin amfani da karfi domin murkushe 'yan IPOB.

Labarai masu alaka