Buhari ya damu da kashe sojojin Najeriya a Borno

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana matukar kaduwarsa game da kisan da aka yi wa sojojin kasar a harin da mayakan Boko Haram suka kai kauyen Metele da ke jihar Borno.

Sai dai ya ce gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen ganin ba a sake maimaita kuskure irin wannan ba wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin.

A cikin sanarwar da Garba Shehu mai bai wa shugaban shawara kan harkokin watsa labarai, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba batun tsaro fifiko domin tabbatar da tsaron lafiyar sojojin kasar da kuma na alummar kasa baki daya.

'Ba bu wani shugaban hafsan hafsoshi da zai zauna wuri daya, ba tare da daukar mataki ba yayin da 'yan ta'ada ke jefa rayuwar sojoji da kuma alumma cikin hadari"

"Dakarunmu sun nuna karfinsu a kan 'yan ta'adda kuma a shirye mu ke mu ba su duk wani goyon baya da suke bukata wajen samar masu da makamai da karin sojoji domin su yi nasara wajen kawo karshen sabuwar barazanar da ake fuskanta daga Boko Haram," in ji shi.

Ya kuma kara da cewa a kwanakin da ke tafe zai tattauna da shugabannin sojoji da kuma na leken asiri a kan matakan da za su dauka.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin internet ya yi ikirarin an hallaka sama da sojoji 100, yayin da kafafen yada labaran kasar suka ce adadin sojojin da aka kashe sun kai 118.

Rundunar sojin Najeriya dai ta tabbatar da kashe sojojin amma ba tare da yi cikakken bayani ba.

A cikin sanarwar, shugaba Buhari ya yi la'akari da cewa yakin da ake yi da 'yan ta'ada ya shafi kasashen duniya shi ya sa ake bukatar hadin kai tsakanin kasashe da ke fuskantar kalubalen tsaron irin wannan.

Ya kuma ba 'yan Najeriya tabbaccin cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen tabbatar da tsaronsu.

Sai dai ya yi kira ga 'yan Najeriya a kan kada su saka siyasa a cikin abin takaicin da ya shafi kasa bakidaya, yana mai cewa mambobin rundunar sojin kasar tsintsiya madaurinki daya ce kuma manufarsu ita ce tabbatar da tsaron lafiyar 'yan kasa baki daya.