Hotunan yadda ake tsiren naman Kwado a Abuja

Tsiren Kwado
Image caption Tsiren kwado a Abuja

Kamar yadda ake yin tsiren nama haka ake yin na kwadi a Abuja Najeriya.

Wasu sun dauki kwado a matsayin nama inda wasu suka ce yana karin jini da kuma lafiya.

Wani mai tsiren kwadin ya shaida wa wakilin BBC Abdou Halilou cewa daga Sabon Birni a jihar Sokoto suke saro kwadin suna kawo wa suna sayarwa a Abuja.

Ya ce duk karamin tsinke ana sayar da shi naira 100, babba kuma naira 200 zuwa 250.

Ana sarrafa shi a tsinke kamar yadda ake yin tsiren naman shanu ko kuma yadda ake jera kaji wajen gashi.

Ya ce a cikin mako daya suna iya sayar da tsinke 500.

Labarai masu alaka