Buhari yana tsoron yin muhawara da Atiku - PDP

Atiku Abubakar na PDP da shugaba Muhammadu Buhari na APC
Image caption PDP na son a yi muhawara tsakanin Atiku da Buhari

Babbar Jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari ya fito a yi muhawara gaba da gaba da dan takararta Atiku Abubakar.

Cikin wata sanarwa, PDP ta ce tana son a yi muhawarar ne kan muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar 'yan Najeriya kafin zaben 2019.

Ta kuma soki Buhari kan batun sojojin Najeriya da Boko Haram ta kashe, inda ta ce "ya yi watsi da sojojin da ke yaki a arewa maso gabas duk da alkawalin da ya yi cewa shi zai jagoranci yaki da Boko Haram."

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da kashe sojojin kasar da Boko Haram ta yi a garin Metele da ke jihar Borno.

Ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan gaggawa wajen ganin ba a sake maimaita kuskure irin wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin ba.

Sai dai kuma a cikin sanarwar da kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya tura wa BBC, jam'iyyar ta ce ya kamata shugaban ya amsa cewa ya gaza, kuma ya shirya tunkarar Atiku kan gazawar da kuma tsarin manufofinsa na gaba domin 'yan Najeriya su auna wanda ya fi dace wa tsakaninsu.

PDP ta ce 'yan Najeriya sun san cewa Buhari yana tsoron ya yi gaba da gaba da dan takararta, Atiku Abubakar a muhawarar da ta ke son wani bangare mai zaman kansa ya jagoranta.

Ta ce wannan wata dama ce ta ba shugaba Buhari ya zabi duk wurin da ya ke so da lokacin da yake ganin ya dace domin tunkarar Atiku a muharawar da ta yi wa dan takarar na jam'iyyar APC mai mulki tayi.