Hotunan bikin nadin Atiku sarautar Wazirin Adamawa

Hakkin mallakar hoto Twitter/@atiku
Image caption An yi bikin nada dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin Wazirin Adamawa na bakwai ranar Lahadi
Hakkin mallakar hoto Twitter/@atiku
Image caption Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na cikin manyan bakin da suka halarci bikin wanda aka yi a Yola, babban birnin jihar Adamawa
Hakkin mallakar hoto Twitter/@saraki
Image caption Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki (dama) na cikin manyan bakin da suka halarci bikin
Hakkin mallakar hoto Twitter/@saraki
Image caption Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan (tsakiya) ya halarci bikin
Hakkin mallakar hoto Twitter/ @YakubDogara
Image caption Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara (tsakiya) da sanata Nazifi Gamawa(dama) da kuma tsohon shugaban hukumar kare hadurra ta kasar, Osita Chidoka (hagu) wurin nadin sarautar Alhaji Atiku Abubakar
Hakkin mallakar hoto Twitter/@benmurraybruce
Image caption Sanata Ben Murray Bruce (na dama a tsaye) a wurin bikin nadin sarautar Alhaji Atiku Abubakar
Hakkin mallakar hoto Twitter/ @YakubDogara
Image caption Manyan baki a jere wurin nadin sarautar Wazirin Adamawa na bakwai
Hakkin mallakar hoto Twitter/@basheer_is1
Image caption Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin da ya sauka a filin jirgin birnin Yola domin halartar bikin nadin Wazirin Adamawa

Labarai masu alaka