Abubuwa biyar da za su faru a wannan makon a duniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron sun halarci taron manema labarai tare da yarima Mohammed bin Salman a fadar Elysee Palace ia ranar 10 ga watan Afirilu 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammed bin Salman tare da Emmanuel Macron cikin annashuwa a watan Afirilu da ya wuce

Yau ranar Litinin ce, rana ta farko a wannan makon, don haka a yayin da muke yin kamar ba mu san dukkan abubuwan da za su faru a makon ba, to lallai ya kamata mu dan yi hasashen wasu abubuwan da za su faru cikin kwanaki bakwai din makon masu zuwa.

Ga dai wasu abubuwa masu muhimmanci da ake sa ran za su faru a duniya a wannan makon.

1)Zafin kai a taron G20

Me zai faru?

A ranar Juma'a mai zuwa ne za a yi taron koli na kasashe 20 masu karfin tattalin arziki wato G20 a birnin Buenos Aires.

Me ya sa aka damu da taron?

A ko da yaushe ba ka rasa babban taron kolin kasashen G20 da wani batu da za a tattauna akai, a shekarar da ta gabata kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ke janyo ce-ce-ku-ce na daga cikin abin da ya mamaye taron. Amma a wannan karon da alama wani batun ne na daban zai taso.

Ta yiwu Yarima Muhammad bin Salman na masarautar Saudiyya zai halarci taron. Sai dai hakan za ta faru ne a daidai lokacin da ake zarginsa da hannu a kisan fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi.

Idon duniya ya raja'a ne a kan shugaban Amurka Donald Trump kan matakin da ya kamata a dauka kan yariman, amma ba lallai hakan ta faru ba.

Baya ga shugaba Trump da zai halarci taron, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta halarta, wadda tana daya daga cikin shugabannin da kai tsaye suka ce lallai ya kamata Saudiyya ta bayyanar da gaskiyar abin da ya faru da Khashoggi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron shi ma zai halarci taron, da tuni kasarsa ta sanyawa mutanen da ake zargi da hannu a kisan dan jaridar takunkumin shiga kasarsa.

Sai kuma mai gayya mai aiki wato shugaban Turkiyya Racep Tayyep Erdogan, da a cikin kasarsa aka kashe dan jaridar daga kuma kasarsa ne aka fara nunawa Saudiyya yatsa kan batun shi ma zai halarta.

Kai shugabannin kasashen duniya daban-daban ne za su taru, kuma yawancinsu ba za su so hotunansu tare da Yarima Bin Salman su zagaya duniya ba, ko zama wuri guda don tattaunawa kan wani batu.

2) Rashin wuta a wani tsibiri?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Me ke faruwa?

Zuwa karshen makon nan za a kashe wutar lantarkin da ke Tsuburin Sark.

Saboda me za a aikata hakan?

Kusan mutane 500 ne ke rayuwa a Tsuburin Sark, kuma wani jami'i a yankin ya ce dole a dauki mataki a cikin makon nan.

A ranar Juma'a mai zuwa ma'aikatan gidan lantarkin yankin za su dakatar da aiki, hakan bai rasa nasaba da umarnin da aka ba su na rage farashin wutar lantarki a shekarar nan ba, lamarin da ya janyo suka rasa makudan kudaden gudanar da kamfanin.

Akwai damuwa matuka ga mazauna yankin, kuma ta yiwu ba su da wani zabi baya ga ficewa daga gidajensu, abin da ake fatan ba zai faru ba.

Amma dole su nemawa kansu mafita ta kowacce fuska don samun wutar lantarkin ciki har da samar da injinan ba da hasken wuta na wucin gadi.

3) Hankula za su karkataa Mississippi

Saboda me?

Makwanni uku kenan da yin zaben tsakiyar wa'adin mulki a Amurka amma har yanzu tsugune ba ta kare ba.

Al'umar Mississippi sun kada kuri'a ne don zabar daya daga cikin 'yan majalisa biyu da suke da su amma abin mamakin babu wanda ya samu isassun kuri'un da zai tsallaka tudun mun tsira, don haka sai an sake gudanar da zaben.

Mecece manufar hakan?

Bayan kammala zaben, jam'iyyar Republican ta samu kujeru 49 a majalisa, yayin da Democrat ta samu 43.

Duk yadda sakamakon zaben da za a sake ya zo a ranar Talata, jam'iyyar Rreplican za ta ci gaba da zama a sahun gaba a majalisar.

Amma idan har Democrat ta yi nasarar kawo kujerar dan majalisa a Mississippi, to za a dan dagulawa Shugaba Trump lamari ta fuskar maunufofin gwamnatinsa.

'Yar majalisar Republican Cindy Hyde-Smith, za ta sha mamaki saboda dogaro da ta yi ga kuri'un bakaken fata Amurkawa to amma a makwannin da suka gabata ta dagulawa kanta lissafi.

Da farko dai an wallafa wani bidiyonta tana raha da wasu mutane biyu da ba sa goyon bayanta kan yunkurin hana su yin rijista amma cikin raha.

Mutumin da take rahar da shi Mike Epsy shi ake sa ran zai zama bakar fata na farko da ya nemi kujerar dan majalisar dattijai a Mississippi.

Duk da ana tababa kan nasarar Epsy, ana ganin kamar Shugaba Trump zai kai ziyara garin don bai wa dan takarar jam'iyyarsa kwarin gwiwa.

4) Sauyin Yanayi

Me zai faru a taron da za a fara kan sauyin yanayi?

Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da taro a karo na 24, don tattauna matsalar sauyin yanayi da za a gudanar a Katowice, na kasar Poland a ranar Lahadi mai zuwa.

Wanne muhimmanci taron ya ke da shi?

Idan mukai waiwaye a shekarar 2015 a wani mataki mai cike da tarihi da shugabannin kasashen duniya suka amince da yin garanbawul na daukar matakan rage sauyin yanayi.

Shekaru uku bayan nan aka fara fadi tashin ganin an fara amfani da matakan a halin da ake ciki ana fatan zaman tattaunawar ta Katowice za ta ciyar da shi gaba.

Ga kasashen da suka ci gaba, batun samar da kudaden da za a magance sauyin yanayi ne a sahun gaba a yanzu.

An fuaskanci cikas da maida hannun agogo baya a lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar baki daya.

Sai dai bayanan da suke fitowa a halin yanzu na cewa ta yiwu shugaba Trump na shirin sauya shawara ta hanyar amfani da damar taron dan tattaunawa kan batun.

50 Dan damben Boxing na ajin babban nauyi Deontay Wilder

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Me zai faru a Amurka?

Danban kasar ajin babban nauyi Deontay Wilder zai fafata da Tyson Fury a ranar Lahadi mai zuwa.

Me hakan ke nufi?

Idan har kai ma'abocin wasan damben Boxing ne za ka gane wannan babban wasa ne da za a kara tsakanin zakaran dambe na ajin babban nauyi da ya dade ya a haskawa a duniyar wasan dambe.

Sannan za a yi karawar ce da daya fitaccen dan wasan damben da shi ma tauraronsa ke haskawa kuma duk wanda ya yi nasara a cikin 'yan wasan biyu zai fuskanci gagarabadau a fagen baki daya wato Anthony Joshua, wanda shi ke rike da sauran kambun zakaru na duniya baki daya.

Idan dan wasa Fury ya yi nasara a wasan da za a kara a birnin Los Angeles din Amurka, hakan zai sharewa dan wasan hanyar kai wa gaci a wasanninsa na gaba.

Labarai masu alaka