Abinci mai guba ya kashe dalibai mata a jihar Kebbi

Kebbi Hakkin mallakar hoto Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya bayyana alhininsa game da rasuwar wasu dalibai mata su uku bayan da suka ci abinci mai guba a makarantar sakandire ta mata da ke Mega a karamar Danko/ Wasagu.

Gwamnan ya nuna matukar kaduwarsa kan lamarin lokacin da ya kai ziyara makarantar sakadiren.

Ya kuma yi kira ga sauran dalibai da su dauki lamarin a matsayin wani abu da Allah ya kaddara kuma su ci gaba da karatunsu.

Kamfanin dilancin labarai na Najeriya NAN ya ambato shugabar makarantar, Lami Abubakar, tana cewa 'yan matan sun ci abinci da iyayen daya daga cikinsu suka kai musu daga gida.

"Daya daga cikin iyayen daliban sun kai wa diyyarsu rama a lokacin da ake barin iyaye su kai ziyara makaranta,kuma ana kyautata zaton cewa gurbattacen abinci ne," in ji ta

Hajiya Lami ta kuma ce daliban sun yi kwana uku a jere suna cin rama kafin suka soma rashin lafiyar da ya yi sanadiyyar mutuwarsu bayan an kwantar da su a asibiti.

Hakkin mallakar hoto Kebbi State Govt
Image caption Daliban sun rasu gamu da ajalinsu ne bayan da suka abinci mai guba

Labarai masu alaka