Abin da ya sa ake kira na "Dankwali" —Aicha Dankwali
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Abin da ya sa ake kira na Dankwali —Aicha Dankwali

Aichatou Ali Soumaila ce jagorar kungiyar mawaka ta Sogha Niger, wacce ta yi fice ba kawai a kasar Nijar ba har ma da makwabta. A kwanan baya aka shigar da kungiyar Majalisar Kungiyoyin Mawaka ta Nahiyar Afirka.

Sai dai kafin nan Aichatou, wacce aka fi sani da sunan Aicha Dankwali ta yi wa BBC bayani a kan wake-waken kungiyar, kuma ta fara ne da bayyana abin da ya sa ake kiranta "Aicha Dankwali."

Amma tun da an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi, latsa alamar lasifikar da ke hotonta don jin bayani daga bakinta.