Sabon samfurin akwatin gawa mai ban mamaki a Ghana

Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu
Image caption Akwatin gawa samfurin motar alfarma ta Marsandi

Al'umar kasar Ghana sun fara sassaka akwatunan gawa wadanda ke tafiya da yanayin da ake ciki na rayuwa, da mafarkan da wasu daga al'uma ke yi, kai har da yadda wasu ke son yanayin bikin binne su ya kasance a lokacin da suka kwanta dama.

'Yan uwa da masoyan mamaci sun yi amannar cewa ya kamata a yi ban kwana da shi cikin wani yanayi mai ban sha'awa da faranta rai.

Wasu 'yan jarida biyu, Fellipe Abreu da Henrique Hedler sun kai ziyara wajen aikin kafinta mai suna Kane Kwei Carpentry Workshops, da ke birnin Accra da kuma dayan da ke kudancin birnin Kumasi, domin ganawa da kafintocin da suka kware wajen kera akwatin gawa na alfarma.

An sanya wa wuraren biyu sunan marigayi Seth Kane Kwei, wanda 'yan kasar suka yi amannar cewa shi ne na farko a kasar Ghana da ya fara yin akwatin gawa irin wannan.

65835 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu
Image caption Akwatin gawa nau'in Cocoa

Kasancewar kasar Ghana na sahun gaba a duniya wajen samar da Cocoa, iyaye da 'yan uwa a yankunan karkara kan tara kudin da suka samu da guminsu domin a binne mamaci a cikin akwatin gawa samfurin cocoa.

Irin wannan akwati kan lakumewa manoma wadanda da kyar suke samun dala daya a kowacce rana, amma suna iya tara sama da dala 1,000 kwatankwacin Naira 360,000.

65788 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu
Image caption Akwatin gawa nau'in tattasai

Wani kafinta mai suna Eric Adjetey da ya kai sama da shekara 50 yana sassaka akwatunan gawa, ya bayyana cewa yanayi ko samfurin akwatin gawar da ake yi wa mamaci, shi ke nuna inda ya fito. Misali idan aka ga akwatin gawa nau'in tattasai ta hakan alama ce ta mamacin manomi ne.

Haka kuma launin Ja da ya ke jikin tattasai shi ma ana alakanta shi da mutum mai zafin rai, irin mutanen da ba sa barin kar-ta-kwana.

Coffin Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu
Image caption Motar alfarma

Amma akwatin gawar da aka yi samfurin motar alfarma ta Marsandi masu hannu da shuni ne ke amfani da ita a kasar Ghana.

Duk mamacin da aka yi wa irin wannan akwatin ya na nuna lallai mai kudi ne, kuma za a haka kabarinsa daidai yadda motar akwatin gawar za ta shige.


Presentational grey line

Yawancin mutane na kiran akwatunan gawa da aka yi su irin haka da na kawa ko na 'yan birni, amma ainahin sunan da ake kiran irin akwatin a kasar Ghana shi ne''Abeduu Adekai'' hakan na nufin ''akwatin alfarma".

Hakan ba ya rasa nasaba da kowanne nau'in akwati akwai abin da yake nufi.

65771 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu

Nau'in jirgin sama shi ma sananne ne a kasar, yawanci an fi yi wa yara kanana inda hakan ke nufin zai isa duniyar mamata cikin nasara.

Yawanci shugabannin al'uma kan taimaka wa 'yan uwan mamaci da dan wani abu dan su samu sayo akwati irin wannan.

65794 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu
Image caption Akwatin gawa samfurin gidan alfarma

A shekarun baya-bayan nan, an fara yin akwatunan gawa samfurin gidajen alfarma saboda yadda wannan fanni ke kara bunkasa a kasar. Wannan akwatin gawa na wani mutum ne da ya mallaki gidajen haya kuma ya na saukakawa 'yan haya kudi domin haka suke ganin shi da kima.

A takaice, alhakin jama'a da 'yan uwa ne su biya kudin da za a yi wa mamaci akwati, sannan su biya kudaden da za a kashe wajen bikin binne shi ciki har da abinci, da kayan sha da sauransu.

Ana gudanar da irin wannan biki ne daga ranar Alhamis zuwa Litinin. A ranar alhamis 'yan uwan mamaci suke kawo akwatin, a ranar Juma'a kuma sai a kawo gawar mamaci daga asibiti, a ranar Asabar sai a yi bikin binne gawar, ranar Lahadi 'yan uwa da abokan arziki za su taru a coci domin yin addu'a.

A ranar Litinin 'yan uwa suke zama domin kidaya kudin da aka tara a zaman makoki dsaboda su zuba su a wani wurin da mamacin zai dinga samun lada.

65756 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu

Kafintoci sukan fitar da siffofi daban-daban na akwatunan gawar, misali akwati mai siffar lasifika ana alakanta shi da mawaka.

Wani kafinta mai suna Mista Ansah ya ce yawanci ba sa sanin tsaho da fadin mamaci domin haka sai su tambayi 'yan uwansa ko kuma a ba su hoton mamacin ta haka suke samun girma da fadin akwatin da za su yi.

65704 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu

A hankali sai sauran kafintocin kasar Ghana su ma suka fara kwaikwayon samfurin akwatin gawar da a halin yanzu bukatarsa kullum ke karuwa.

65098 Hakkin mallakar hoto Fellipe Abreu

Nau'in zane da kirar da ake yi mai siffar sarauniya, masu kere-kere da zane-zanen yankin Philadelphia a Amurka ne suka fara samar da shi.

Amma daga baya aka mayar da shi akwatin gawa, kuma sama da shekaru 10 ke nan da mutane daga kasashe kusan 20 suka fara zuwa da shi domin binne mamata.

Kafintoci na amfani da sassaukar hanya wajen fitar da suffar abin da ake bukata kuma daga bisani ya zama akwatin gawa.

Presentational grey line

Ansamo wadannan bayanai da hotuna daga 'yan jaridar da suka yi bincike a kai - wato Fellipe Abreu da Henrique Hedler.

Labarai masu alaka