Mata 100: 'Mata 137 makusantansu ke kashe su kullum a duniya'

An average of 137 women across the world are killed by a partner or family member every day

Wasu sabbin bayanai da Ofishin hana shan kwayoyi da aikata miyagun laifuka na Majalisar Dinkin Duniya UNODC ya fitar sun ce a kalla mata 137 ake kashewa a kowace rana a fadin duniya, kuma 'yan uwan matan ko abokan tarayyarsu ne ke kashe su.

Sun ce an mayar da gidaje "wajen da aka fi kashe mata."

Rahotannin sun ce fiye da rabin mata 87,000 da aka kashe a shekarar 2017 yawancimakusantansu ne suka kashe su.

A kan wannan adadin, a kiyasce mata 30,000 ne abokan taryyarsu suka kashe, inda mata 20,000 kuma 'yan uwansu ko danginsu ne suka kashe su.

Short presentational grey line

Shirin Mata 100 na BBC ya so gano su waye matan da irin haka ta shafa. Mun shafe watan Oktoba muna bibiyar rahotanni kan kashe-kashen da suka shafi jinsin mata tun ranar farko ta wannan watan.

Za mu nuna muku wasu labaransu a kasa don ku san yadda kisan nasu ya gudana.

kashe-kashen mata a duniya

Kin jinin maza na karuwa

Bayanan da UNODC ya tattaro ya nuna cewa "maza sun fi fuskantar hatsarin rasa rayuwarsu sau hudu fiye da mata a sakamakon kin jininsu da gangan."

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa maza ne suka fi fuskantar hatsrain kin jini kashi takwas daga cikin 10 a duniya.

Sai dai kuma, wannan rahoton ne ya nuna cewa takwas daga cikin 10 na wadanda makusantansu suka fi kashewa saboda kin jini mata ne.

Rahoton ya bayyana cewa: "Rikici tsakanin abokan hulda makusanta na ci gaba da zama barazana ga mata."

kashe-kashen mata a duniya

Mata saba'in da daya, kasashe 21, a rana guda

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta fayyace abun da aka gano na shekarar 2017 kan batun kin jinin jinsi wanda majiyoyin gwamnati suka gabatar.

An tattaro alkalumma kan kisan mata ko yara mata na kin jinin jinsi da makusantansu suka aikata.

Shirin Mata 100 na BBC da kuma bangaren BBC da ke nemo labarai daga wasu wuraren wato BBC Monitoring, sun shirya tsaf don gano irin wadannan matan da kuma yawansu.

Mun bibiyi wani taron manema labarai na matan da aka kashe da aka yi ranar 1 ga watan Oktobar 2018 a fadin duniya.

Kwararrunmu na sassa daban-daban sun lissafa mata 47 da aka ruwaito cewa an kashe, yawanci saboda dalilai da ke da alaka da jinsi a kasashe 21 daban-daban. Yawanci ana binciken kisan.

Ga dai wasu labarai biyar na irin hakan, wadanda da fari kafafen yada labaran kasashen da suka faru ne suka ruwaito amma daga bisani hukumomin kasashen sun tabbatar da hakan kuma BBC ta tuntube su.

Judith Chesang Hakkin mallakar hoto Family handout

Judith Chesang, mai shekara 22 'yar Kenya

Ranar Litinin 1 ga watan Oktoba, Judith Chesang da 'yar uwarta Nancy suna gona suna nome dawarsu.

Judith na da 'ya'ya uku kuma ba a jima ba da suka rabu da mijinta Laban Kamuren, sai ta koma wajen iyayenta a wani kauye da ke arewacin kasar.

Jim kadan bayan da kannenta suka fara aikin, sai ya lallabo gonar tasu ya kashe Judith.

'Yan sandan yankin sun ce tuni 'yan kauyen suka kashe shi.

kashe-kashen mata a duniya

Rahoton MDD ya ce "Afirka nan ne inda mata suka fi fuskantar barazanar kisa daga makusantansu ko 'yan uwansu.

Yankin Asiya ne aka fi samun yawan kashe mata da 'yan uwansu ko makusantansu ke yi a 2017, inda jumullar hakan ta kai 20,000.

Neha Chaudhary Hakkin mallakar hoto Manohar Shewale

Neha Sharad Chaudury mai shekara 18 'yar Indiya

Neha Sharad Chaudury ta mutu ranar bikin cikarta shekara 18. Ta fita ne tare da saurayinta don murnar bikin cikarta shekara 18.

'Yan sanda sun tabbatar wa da BBC cewa iyayenta ba sa son mu'amalarta da saurayin.

An zargi iyayenta da wani dan uwanta da kashe ta a gida a wannan yammacin.

Ana ci gaba da binciken kuma 'yan uwanta na hannun hukuma suna jiran hukunci.

Lauyan da ke wakiltar Neha ya shaida wa BBC cewa iyayenta da wannan dan uwan nata suna so su karyata zargin da ake musu.

Daruruwan mutane ake kashewa a kowace shekara sakamakon soyayyar da suke fadawa wacce iyayensu ba sa so ko danginsu.

Zai yi wahala a samu adadi a hukumance na irin wannan kisa da ake yi saboda yadda ya yi yawa kuma ba a adana bayanan.

Zeinab Sekaanvand Hakkin mallakar hoto Private via Amnesty International

Zeinab Sekaanvan mai shekara 24, 'yar Iran

Hukumomin Iran ne suka zartar da hukuncin kisa a kan Zeinab Sekaanvan saboda kashe mijinta da ta yi.

An haifi Zeinab ne a arewa maso yammacin Iran, kuma ta fito ne daga wata zuri'a ta talakawa masu tsaurin ra'ayi a kabilar Kurdawa. Ta gudu a lokacin da take matashiya don ta yi aure a inda take ganin za ta samu rayuwa mai kyau.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce mijinta yana cin zalinta kuma ya ki sakinta, sannan kuma 'yan sanda sun ki su saurari kukanta.

An kama ta saboda kashe mijinta a lokacin da take da shekara 17.

Masu goyon bayanta ciki har da Amnesty, sun ce an azabtar da ita don ta amince cewa ita ta kashe mijinta, inda 'yan sanda suka yi ta dukanta kuma suka ki yi mata adalci a shari'ar.

Rahoton hukumar UNODC ya ce matan da suke kashe abokan tarayyarsu sun fi shan wahala sosai wajen azabtar da su da ake yi.

A hannu guda kuma abun da ya sa mazan da ke aikata irin haka suke wannan abu sun hada da "mallaka da kishi da kuma tsoron kar matan su daina yayinsu, a cewar rahoton.

Wannan ne irin abun da ya faru ga wasu ma'aurata da aka gano su a mace a Brazil a ranar da aka kashe Zeinab.

Sandra Lucia Hammer Moura Hakkin mallakar hoto Reproduction / Facebook

Sandra Lucia Hammer Moura mai shekara 39, 'yar Brazil

Sandra Lucia Hammer Moura ta auri Augusto Aguiar Ribeiro lokacin tana 'yar shekara 16.

Ma'auratan sun rabu tsawon wata biyar a lokacin da mijin ya kashe ta.

'Yan sanda a Jardim Taquari sun tabbatar wa da BBC Brasil cewa a wuyanta aka caka mata wuka.

Sun gano wani bidiyo a wayar salula inda mijinta yake ikirarin daukar alhakin kisa.

A cikin wayar salula ya fadi cewa ai Sandra tana mu'amala da wani namijin, sai yake jin cewa ta ci amanarsa.

Marie-Amélie Vaillat Hakkin mallakar hoto PHOTOPQR/LE PROGRES/Photo Jean-Pierre BALFIN

Marie-Amélie Vaillat mai shekara 36, 'yar Faransa

Marie-Amélie ta mutu ne sakamakon daba mata wuka da mijinya Sébastien Vaillat ya yi.

Ma'auratan sun rabu ne bayan sun shekara hudu da aure.

Ya kai mata hari da wuka kafin ya bayyanawa 'yan sanda gaskiyar lamarin. Kwanaki kadan bayan nan sai ya kashe kansa a gidan yari.

Kisan Marie-Amélie ya zo ne a ranar da gwamnatin Faransa ta sanar da sabbin shirye-shirye na kawo karshen rikici tsakanin ma'aurata.

A march in memory of Marie-Amélie Vaillat Hakkin mallakar hoto PHOTOPQR/LE PROGRES/Photo Jean-Pierre BALFIN
Image caption An yi maci don tunawa da Marie-Amélie Vaillat
Short presentational grey line

Ta yaya za a bayar da rahoton kisan mata?

Domin tattara wadannan labaran, ma'aikatan BBC Monitoring na kasashen duniya da masu bincike sun fayyace labarai na talbijin da rediyo da jaridu da intanet da kafafen sada zumunta a fadin duniya, inda suke neman rahotanni kan matan da aka kashe saboda abun da ya shafi jinsi, a ranar 1 ga watan Oktoban 2018.

Sun gano jumlar rahotanni 47 na matan da aka kashe a rana guda a fadin duniya. Mun yada kadan daga cikin wadannan labarai. Akwai wasu labaran da dama da ba mu gama tabbatar da yadda abun ya kasance ba ko kuma ba a gano wadanda suka aikata hakan ba.

Sabon rahoton UNODC ya ce ba a faye yada rahotannin cin zarafin da ake yi wa mata ba, kuma ba a faye sanar da hukumomi ba, ko kuma ana boye irin wadannan al'amura.

Rebecca Skippage wacce ta jagoranci BBC Monitoring ta gano cewa a bayan yawan mutanen da abun ke shafa, "yadda kafafen yada labarai ke bayar da rahoton rayuwa da mutuwarsu na bayyana girman yadda kowace al'umma ke kallon mata a fadin duniya."

Ta bayyana cewa: "Muna neman mace-macen da suka faru a rana guda, amma ya dauke mu tsawon wata daya neman wannan labari. Mun gano cewa ba a samun wadannan bayanai ko rahotanni kan abun da suka shafi mata a wancan yankin."

Maryam Azwer ita ma tana aiki da BBC Monitoring kuma da ita aka gano wasu bayanan.

"Kwanakin da ake bayar da rahotannin abubuwan da ke faruwa, sun nunka na wadanda ba a bayar ba," in ji ta.

"Wadanda labaransu ba su kai ga kafafen yada labarai ba, wadanda ba a ba da rahotanninsu ba, ko kuma ba a yi bincike ba. Abun zai ba ku mamaki cewa: wane abu ne zai sa a dauki kisan mace da muhimmanci sosai ta yadda za a bayar da rahotonsa?"

Short presentational grey line

Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka

Wacce ta dauko rahoto: Krupa Padhy

Shiryawa: Georgina PearceResearch: BBC Monitoring

Tsare-tsaren kididdiga cikin hotuna: Christine Jeavans and Clara Guibourg. Design: Zoe Bartholomew. Development: Alexander Ivanov

Mene ne Shirin Mata 100 na BBC?

BBC 100 Women na zabar sunayen mata 100 sannanu masu tasiri a sassa daban-daban na duniya kowace shekara, sai kuma a ba da labarinsu.

Wannen shekarar ta yi tasiri sosai a kan kare hakkokin mata a duniya, Saboda haka a 2018 Shirin Mata 100 na BBC zai haska rayuwar matan da suka shige gaba wajen amfani da hazaka da fushinsu wajen kawo sauyi a tsakanin al'ummominsu.

Za ku iya samun mu a shafinmu na Facebook da Instagram da na Twitter da hanyar amfani da mau'du'in #100Women

Labarai masu alaka