Najeriya 'ta yi asarar' dala biliyan shida a yarjejeniyar fetur

Kamfanin hako mai a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin Shell da Eni da rashawa a Najeriya

Wata kotu a Italiya na tuhumar kamfanin hako mai na Eni da Shell da zargin rashawa a yarjejeniyar cinikin danyen mai wanda har ya kai ga Najeriya yin sarar kudi kimanin dala biliyan shida.

Batun da ke gaban kotun Milan, an bayyana cewa ya shafi tsohon shugaban Najeriya wanda ba a bayyana sunansa ba da kuma wasu tsoffin manyan jami'an kamfanin mai na kasar.

Yarjejeniyar ta ba Shell da Eni 'yancin gano wata cibiyar mai a yankin Neja Delta wadda aka kiyasta tana dauke da kimanin biliyan tara na gangar mai.

Ana zargin akwai rashawa a hanyoyin da suka bi wajen samun kwangilar.

An zargi Shell da Eni cewar sun biya gwamnatin Najeriya dala biliyan $1.1 maimakon sun san cewar za a karkatar da kudaden ga cin hanci da rashawa.

Sai dai kamfanonin guda biyu na Italiya da Holland sun musanta zargin, kuma sun shaidawa BBC cewa wannan bacin suna ne.

Masu fafutika sun yi imanin cewa sakamakon wannan shari'ar a kotun Milan zai bankwado abubuwa da dama a bangaren harkar mai a Najeriya.

Wata kungiyar fafutika da ake kira Global Witness ta yi kiyasin cewa yarjejeniyar ta 2011 da ake kira OPL 245, sun nunka kasafin kudin Najeriya da aka ware wa bangaren ilimi da kiwon lafiya.

Global Witness ta shafe shekaru tana gudanar da bincike game da yarjejeniyar OPL 245 da ta ba Shell da Eni 'yancin hako mai a yankin Neja Delta.

Kuma kungiyar ta ce kudaden sun isa su samar da horo na musamman ga malaman makaratun Najeriya miliyan shida.

Labarai masu alaka