Malamin Islamiyya ya yi wa yarinya 'fyade' a Kano

Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron bayanin da kakakin 'yan sandan jihar Kano ya yi wa BBC:

Rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano ta kama wani malamin Islamiyya mai shekaru 41, bisa zargin bata wata yarinya 'yar shekara takwas.

Yarinyar dai na daya daga cikin wasu yara bakwai da aka dauke shi musamman don ya rika koyar da su ilimin addini gidansu.

Mai magana da yawun reshen rundunar ta jihar Kano, Sufuritenda Magaji Musa Majiya ya shaida wa AbdusSalam Ibrahim Ahmed, cewa sun sami kwararan hujjojin gurfanar da malamin a gaban kuliya, kuma iyayen yarinyar sun yi tsayuwar daka a kan a bi masu hakki.

Ya ce malamin ya yi amfani da wasu dubaru na janyo hankalin yarinyar har ya yi lalata da ita a bayan gidansu.