Buhari ya ce da gangan APC ta tauye hakkin masu son yin takara

Buhari ya ce bai kamata APC ta yi barazana ga masu son kai ta kotu ba Hakkin mallakar hoto Twitter/@OfficialAPCNg
Image caption Buhari ya ce bai kamata APC ta yi barazana ga masu son kai ta kotu ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce da gangan jam'iyyarsa ta APC ta tauye hakkin wasu daga cikin 'ya'yanta da ke son yin takara a zaben 2019.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin da daddare.

Ya goyi bayan 'ya'yan jam'iyyar da suka gurfanar da ita a gaban kotu domin neman hakkinsu sakamakon rashin adalcin da aka yi musu a zabukan fitar da gwanin da jam'iyyar ta yi.

"Ban amince da matsayin jam'iyyarmu ba wacce ta haramta wa mambobin da aka bata wa rai zuwa kotu inda take gargadin ladabtar da su,' in ji Shugaba Buhari.

"Ba zai yiwu da gangan mu tauye hakkin mutane ba. Mun amince mu gudanar da zaben fitar da gwani a hanyar yin ko dai 'yar-tinke ko hanyar wakilai ko kuma yin sulhu tsakanin masu son yin takara, sannan muka amince cewa duk wanda ya ga ba a yi masa adalci ba zai iya zuwa kotu.

"Ya kamata kotu ta kasance wuri na karshe da mutanen da ba su gamsu ba za su nufa. Don haka ba zan amince da yanayin da jam'iyya za ta hana su zuwa kotu ba," in ji Shugaba Buhari.

Da ma dai masu ruwa da tsaki a jam'iyyar, ciki har da mai dakin shugaban kasar, Aisha Buhari, sun soki APC bisa rashin adalcin da suka ce ta yi wa masu neman takara.

Aisha Buhari ta ce "Abin takaici ne wasu 'yan takara sun yi amfanin da kudin guminsu sun sayi fom din takara, sannan an tantance su, kana sun yi yakin neman zabe iya karfinsu, amma kuma an cire sunayensu a ranar zabe."

Ta zargi shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole - mutumin da ta ce an sani da nuna damuwa da kuma kokarin kwatowa talakawa 'yancinsu - da kitsa rashin adalci a APC, ko da yake ya musanta zargin.

Su kansu wasu gwamnonin jam'iyyar, irinsu Abdul Aziz Yari na Zamfara da Ibukunle Amosun na Ogun da Rochas Okorocha na Imo, sun sha sukar shugaban jam'iyyar game da yadda ya gudanar da zabukan fitar da gwanin na APC.

Hasalima, rikicin da ya kaure tsakanin wasu 'yan takarar a jihar Zamfara ya yi sanadin gaza mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisun dokoki ga hukumar aben kasar har wa'adin mika sunayen ya wuce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Buhari ya ce APC ba ta bi ka'idojin zaben fitar da gwani ba

Karanta wasu karin labaran:

Labarai masu alaka