Buhari ya amince a kara wa 'yan sanda albashi

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin 'yan sandan da karbar cin hanci

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce amince a kara wa 'yan sandan kasar albashi.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter kuma ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa 'yan sandan kayayyakin aikin da suke bukata da inganta walwalarsu.

Sai dai ya nuna takaici a kan yadda 'yan sandan suka gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen yaki da masu aikata miyagun laifuka abin da kuma ya sa sojoji suka shigo cikin harkar tabbatar da doka da oda a kasar bakidaya.

"Daga Taraba zuwa Sokoto, har yankin kudu maso kudancin Najeriya, mutane ba su da kwarin gwiwa a kan tsaro idan ba su ga sojoji ba. Ina farin cikin kara albashi da alawus-alawus din 'yan sanda da fatan wannan zai karfafa masu gwiwa tare da inganta tsarin samar da tsaro na cikin gida na Najeriya," in ji Shugaba Buhari.

Shugaban na Najeriya ya ce idan aka samu 'yan sanda masu kwazo sosai, hakan zai karfafa gwiwar gwamnati da al'ummar kasar kan jami'an 'yan sanda.

"Ya kamata a bar sojoji su rika tunkarar manyan matsaloli. Ya kamata 'yan sanda su iya shawo kan kalubalen da ake fuskanta daga wurin masu fashi da makami da masu garkuwa da mutane domin a ba su kudin fansa da sauransu."

Sai dai tambayar da masu sharhi kan lamuran tsaro ke yi ita ce shin karin albashin zai sa 'yan Najeriya su ga sauyi daga wurin 'yan sandan kasar?

Ana zargin 'yan sandan kasar da karbar hanci daga wurin mutane ko matafiya idan suna aikin a kan hanya ko shingayen bincike, ko da yake wasu daga cikin 'yan sanda sun ce wannan na da nasaba da rashin wani abin azo a gani game da albashin da ake biyansu.

Sai dai kuma akwai wasu da ke ganin cewa matsalar ba ta tsaya ne kan kula da walwalar 'yan sandan kawai ba - har d ba su horo da cusa musu da'a.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya ce bai kamata 'yan sanda su rika aiki cikin kuncin rayuwa ba

Labarai masu alaka