Yadda bacci ya dauke direban jirgin sama yana tuki

Direban jirgin saman Hakkin mallakar hoto aviation-images.com
Image caption Direban jirgin saman

Hukumomin da ke kula da lafiyar jirage sun ce wani karamin jirgi da ya kamata ya sauka a Australia ya wuce da gudu bayan direban jirgin ya yi bacci.

Direben jirgin kadai ne wanda ya ke cikin jirgin da ya tashi daga Devonport zuwa King Island zuwa Tasmania a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Hukumar da ke kula da harkokin jiragen sama ta Australia ATSB na gudanar bincike kan al'amarin.

Har yanzu hukumomi ba su bayyana yadda direban jirgin ya sauka daga cikinsa lami lafiya ba.

Image caption Taswira

A shafinsu na intanet, Vortex Air sun ce aikinsu ya shafi daukar shatar jirgin sama ga kungiyoyi da kamfanoni da masu yawon shakatawa a Australia.

Hukumar ATSB sun ce za su tattauna da direban jirgin kuma za su binciki yadda ake tafiyar da jirgin kafin a fitar da rahoton zuwa badi.

Labarai masu alaka