Girgizar kasa ta jikkata mutum 700 a Iran

People look on around the damaged buildings after 6.4 magnitude earthquake that hit western Iran near the border with Iraq, in Tehran, Iran on 26 November 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu gine-gine da girgizar kasar ta shafa a Tehran

Fiye da mutum 700 ne suka ji raunuka bayan da wata girgizar kasa mai karfin maki 6.3 da ta auku a kudancin kasar Iran a ranar Lahadi, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

Girgizar kasar ta fi kamari ne a lardin Kermanshah, a bara ma fiye da mutum 600 ne suka mutu a wata mummunar girgizar kasa a tsawon shekara 10.

An jiyo motsin kasar a yankuna da dama na kasar, inda rahotanni suke cewa a kalla mutum guda ya rasa ransa a kusa da yankin Kurdistan na kasar Iraki.

Sai dai babu rahotannin asarar rayuka a kasar Iran, kuma babu wani rahoto da ke cewa girgizar kasar ta yi wani babban ta'adi.

Gwamnan lardin da abin ya shafa Houshang Bazvand ya ce: "Kimanin mutum 729 ne suka ji raunuka, 700 an yi musu magani har ma an sallame su...18 kuma an kwantar da su a asibiti."

Wani jami'in hukumar Red Crescent a Iran, Morteza Salimi ya shaida wa AFP cewa mutane sun ji raunuka ne bayan wani turmutsitsi da ya auku bayan faruwar motsin kasar.

Image caption Taswira da ke nuna wajen da girgizar kasar ke faruwa

Masu kula da nazarin yanayin kasa na Amurka (USGS) sun ce girgizar kasar ta kai kimanin nisan kilomita 20 daga garin Sarpol-e Zahab, da zurfin kilomita 10, kuma ta faru da kamar karfe 8 na dare agogon kasar a ranar Lahadi.

Gwamnan lardin, Houshang Bazvand, ya shaidawa gidan talabijin na kasar a ranar Litinin cewa: "Mun samu mutane 729 da suka ji rauni, an kuma duba mutane 700 kuma aka sake su... an kuma kai mutane 18 asibiti".

Gidan talabijin din ya wallafa bidiyon gidajen da suka rugurguje a Sarpol-e Zahab, inda mutane da dama har yanzu ba su da muhalli saboda girgizar kasa da ta afku a bara.

Hukumomi sun ce an tura kungiyoyin ceto da dama, da kuma sojojin kasa da kuma masu kare juyin juya hali na Iran.

Gidan talabijin din ya ce: Shugaban kasar Hassan Rouhani "ya umarci jami'ai su yi duk abin da ya kamata don samar da taimako ga wadanda al'amarin ya shafa".

Mazauna birnin Baghdad da ke kasar Iraki- mai kimanin nisan kilomita 175 - da kuma wasu larduna da ke Iraki sun ji motsin girgizar a ranar Lahadi.

An tilasta mutane da yawa a cikin yankunan da girgizar kasar ta shafa su kwana a waje cikin sanyi saboda damuwa da tashin hankali da suka shiga bayan abun da ya same su.

Iran tana wani waje da ake yawan samun girgizar kasa a duniya. A shekarar 2013, an samu wata gagarumar girgizar kasa mai maki 6.6 da ta lalata birnin Bam mai tarihi a kudu maso gabashin kasar, inda ta kashe mutane 26,000.

Labarai masu alaka